“Kasuwa Bata Yi Kyau Ba”: Gwamna Samuel Ortom Ya Magantu Kan Kayen Da Ya Sha a Zaben Sanata

“Kasuwa Bata Yi Kyau Ba”: Gwamna Samuel Ortom Ya Magantu Kan Kayen Da Ya Sha a Zaben Sanata

  • Gwamna Samuel Ortom na jihar Benue ya bayyana cewa bai kwasheta da dadi ba a kudirinsa na son zama sanata a zaben 2023
  • Gwamnan ya ce zai mayar da hankali ga harkar noma bayan mika mulki ga magajinsa a ranar 29 ga watan Mayu
  • A cewar Ortom, gwamnonin G5 na PDP sun cimma muradin mambobinsu da mutuncin kungiyar

Gwamnan jihar Benue, Samuel Ortom ya bayyana cewa 'kasuwa bata yi masa kyau ba' a zaben 2023 da aka kammala, jaridar Punch ta rahoto.

Ortom, zababben gwamnan jihar Benue ya yi takarar kujerar sanata mai wakiltan Benue ta arewa maso gabas karkashin inuwar jam'iyyar Peoples Democratic Party (PDP).

Gwamna Samuel Ortom na jihar Benue
“Kasuwa Bata Yi Kyau Ba”: Gwamna Samuel Ortom Ya Magantu Kan Kayen Da Ya Sha a Zaben Sanata Hoto: Vanguard
Asali: UGC

Kalmar 'kasuwa bata yi dadi ba' da Ortom ya yi amfani da shi a kan yi amfani da shi ne don nuna cewa abun da mutum ya sanya gaba bai tafi yadda aka so ba.

Kara karanta wannan

Buhari Ya Zolayi Gwamnoni Da Suka Sha Kaye A Zaben Sanata, Ya Aika Sako Ga Yan Siyasa

Zan koma ga gonata bayan mika mulki, Ortom

Da yake magana kan kayen da ya sha a zaben Sanata yayin da ya bayyana a shirin Arise TV a ranar Juma'a, 7 ga watan Afrilu, Ortom ya ce fatansa na son zama dan majalisar Najeriya ya zama mafarki lokacin da ya sha kaye a hannun tsohon hadiminsa, Titus Zam.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Ya kuma ce da wannan kayen da ya sha a zaben sanata, shakka babu yana iya komawa gonarsa ko ya samu wani abun yi bayan ya mika mulki ga gwamnati mai zuwa a ranar 29 ga watan Mayu.

Kalamansa:

"Kasuwar (takarar sanata) a gareni bata yi kyau ba. A wannan karon, kasuwar bata yi dadi ba amma zan kasance a nan (a matsayin gwamnan Benue) har zuwa ranar 29 ga watan Mayu lokacin da zan mika mulki da izinin Allah zan nemi wani abun yi. Ina iya komawa ga gonata a iya sanina.

Kara karanta wannan

An matsa mani lamba: Bayan tono asirinsa, Peter Obi ya fasa kwai game da zaben 2023

"Ni da sauran (Gwamnonin G5) mun yi nasarar cimma muradin mambobinmu, kungiyar mutunci. Saboda G5 sun fito ne sakamakon zaben fidda gwanin PDP da kuma babban taron jam'iyyar na 2022. Wasu sun yarda da mu cewa ya kamata a mika mulki zuwa wani yankin."

"Duk wanda bai gamsu ba ya tafi kotu neman gyara": Buhari ga Atiku, Obi da sauransu

A wani labarin, mun ji cewa shugaban kasa Muhammadu Buhari ya bukaci wadanda suka fadi zaben 2023 kuma basu gamsu da sakamakon ba da su tafi kotu sannan su yi hakuri doka ta yi aikinta yadda ya kamata.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Musa avatar

Aisha Musa (Hausa writer) Aisha Musa 'yar jarida ce wacce ta kwashe shekaru biyar tana aikin gogewa a harkar yada labarai. Ta kammala karatun ta a Jami'ar Ibrahim Badamasi Babangida (IBB Lapai) a shekarar 2014 tare da digirin farko a fannin Tarihi. Aisha Editan Hausa ce wacce ke amfani da kwarewa da kwazonta don karfafawa wasu gwiwar yin aiki tukuru don cimma nasara. Ta karbi lambar yabo na gwarzuwar shekarar 2021 a bangaren Hausa na Legit. Za ku iya aika mata sakonnin imel ta adireshinta aisha.musa@corp.legit.ng