Duk Wanda Zaben 2023 Bai Masa Daɗi ba Ya Hakura Ya Tari Gaba, Sanata Adeyemi
- Sanatan jam'iyyar APC daga jihar Kogi, Smart Adeyemi, ya ce zaben da aka kammala bai da wani aibu kuma ba'a taba kamarsa ba
- Adeyemi ya shawarci waɗanda zaben ya yi musu ɗaci da su ɗau dangana su tari zabe na gaba
- Bola Tinubu ne ya ci zaɓen shugaban kasa amma Atiku da Peter Obi sun ce sam ba su yarda ba kuma sun garzaya Kotu
Sanata Smart Adeyemi, ya ayyana babban zaɓen 2023 da aka kammala a matsayin wanda ba'a taba yin sahihi kamarsa ba a ƙasar nan.
Mista Adeyemi ya yi kira ga 'yan takarar da sakamakon zaɓen bai musu daɗi ba da su zuba wa zuƙatansu ruwan sanyi su tari gaba.
Sanata Adeyemi daga jihar Kogi, mamba a jam'iyyar APC, ya yi wannan furucin ne a cikin shirin Politics Today na Channels tv ranar Alhamis.
Idan zaku iya tunawa, Bola Tinubu na APC ne ya lashe zaben shugaban ƙasa da aka kammala amma manyan abokan karawarsa kamar Atiku Abubakar na PDP da Peter Obi na LP sun kalubalanci sakamakon.
DUBA: Bibiyemu a Instagram don samun labarai masu muhimmanci kai tsaye cikin manhajar
Amma da yake tsokaci kan babban zaɓen, Sanata Adeyemi, ya ce zaben na ɗaya daga cikin mafi sahihanci da aka taba gudanarwa a tarihin Najeriya duk da ba za'a ce bai da naƙasu ba.
Smart Adeyemi ya ce:
"A irin wannan lokacin ina faɗin abinda ke cikin raina, maganar gaskiya wannan zaɓen sahihi ne na matakin farko kuma ya fi zaɓukan da muka gudanar a baya. Duk wanda bai ji daɗi ba ya tara a gaba."
Ya kuma yi musun cewa tsohon gwamnan Legas, Bola Tinubu da abokin takararsa, Kashim Shettima su mutane su ka fi aminta su jagoranci ƙasar nan.
"Maganar gaskiya ita ce Asiwaju da Kashim su ne a sahun gaba daga cikin yan takara kuma su suka samu nasara," inji shi.
A cewarsa, fushi daga bangaren yan adawan da suka sha kaye a zabe abu ne da ake tsammani amma ya jaddada cewa an yi sahihi kuma ingantaccen zaɓe.
El-Rufai Ya Yaba Wa Gwamna Wike
A wani labarin kuma El-Rufai Ya Yaba Wa Gwamna Wike, Yace Mutanen Ribas Sun Yi Abinda Ya Dace Da Suka Zabi Tinubu
Gwamnan jihar Kaduna, Malam Nasiru El-Rufai, ya kaddamar da wani aikin gwamna Wike a jihar Ribas, ya yaba masa bisa goyon bayan Tinubu.
Asali: Legit.ng