Rigima Ta Kunno Kai a Jam'iyyar Labour Party, An Yi Wa Shugaban Jam'iyyar Juyin Mulki Rana Tsaka

Rigima Ta Kunno Kai a Jam'iyyar Labour Party, An Yi Wa Shugaban Jam'iyyar Juyin Mulki Rana Tsaka

  • Rigima na cigaba da kunno kai cikin jam'iyyar Labour Party (LP) kan matsalar shugabancin jam'iyyar na ƙasa
  • Mataimakin shugaban jam'iyyar na ƙasa ya bayyana kansa a matsayin sabon shugaban jam'iyyar
  • Hakan na zuwa ne bayan wata kotu ta dakatar da shugaban jam'iyyar na ƙasa daga shugabancin jam'iyyar

Abuja - Mataimakin shugaban jam'iyyar Labour Party (LP) na ƙasa yankin Kudu, Lamidi Apapa, ya bayyana cewa ya karɓe ikon mulkin jam'iyyar, rahoton The Cable.

Sanarwar hakan na zuwa ne bayan shugaban jam'iyyar na ƙasa, Julius Abure, ya yi zargin cewa ƴan daba bisa taimakon jami'an tsaro sun mamayi hedikwatar jam'iyyar da ke birnin tarayya Abuja inda suka lalata kayayyaki da dama.

Labour Party
Rigima Ta Kunno Kai a Jam'iyyar Labour, An Yiwa Shugaban Jam'iyyar Juyin Mulki Rana Tsaka Hoto: Head Topics
Asali: UGC

Sai dai, Abure ya ɗora alhakin mamayar da ƴan daban suka kawo hedikwatar jam'iyyar akan jam'iyyar All Progressives Congress (APC).

Kara karanta wannan

Yanzu-Yanzu: 'Yan Daba Sun Kutsa Kai Cikin Sakatariyar Jam'iyya Ta Ƙasa a Abuja

Da yake tattaunawa da ƴan jarida a hedikwatar jam'iyyar ranar Alhamis, a yayin wani taron gaggawa na kwamitin gudanarwar jam'iyyar na ƙasa, Apapa ya ce ya karɓe ikon mulkin jam'iyyar ne bayan umurnin kotu da ta hana Abure ɗaukar kansa a matsayin shugaban jam'iyyar na ƙasa.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Apapa ya kuma bayyana cewa Saleh Lawan shine sakataren jam'iyyar na ƙasa na riƙo.

Kotun dai ta hana sakataren jam'iyyar na ƙasa Farouk Ibrahim, sakataren tsare-tsaren jam'iyyar na ƙasa, Clement Ojukwu, da ma'ajin jam'iyyar na ƙasa Oluchi Opara, da bayyana kansu a matsayin shugabannin jam'iyyar.

A cewar Lamidi, Abure da sauran mutum ukun dole ne su bi umurnin babban kotun tarayya da ta hana su bayyana kan su a matsayin shugabannin jam'iyyar.

Taron gaggawan na NWC ya kuma mayar da mambobin kwamitin zartarwa na jihohin Ogun, Rivers da Gombe kan muƙaman su, rahoton The Nigeria Lawyers

Kara karanta wannan

Mataimakin Shugaban APC Ya Fasa Kwai Kan Yadda Ake Bayar Da Cin Hanci Don Samun Shugabancin Majalisa

A lokacin taron, Lamidi ya kuma warware dakatarwar da aka yiwa shugaban matasan jam'iyyar na ƙasa, Eragbe Anslem da sakataren watsa labarai na ƙasa na jam'iyyar Yomi Arabambi.

'Yan Sanda Sun Mamaye Sakatariyar Jam'iyyar Labour Party a Imo

A wani labarin na daban hukuma, jami'an ƴan sanda sun mamaye sakatariyar jam'iyyar Labour Party a jihar Imo dake yankin Kudu maso Gabas na Najeriya.

Sakataren jam'iyyar na ƙasa shine ya koka kan wannan mamayar da ƴan sanda suka yi wa sakatariyar jam'iyyar.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sharif Lawal avatar

Sharif Lawal Sharif Lawal ma'aikacin jarida ne wanda ya samu gogewa a harkar aikin jarida. Ya yi digirinsa na farko a jami'ar Ahmadu Bello (ABU) da ke Zaria. Ya samu horo daga Reuters kan aikin jarida da tantance labarai. Za a iya tuntubarsa ta Sharif.lawal@corp.legit.ng