Yan Daba Sun Kutsa Kai Sakatariyar Labour Partya Ta Kasa a Abuja
- Rigingimun cikin gida na jam'iyyar Labour Party sun kara tsananta yau Alhamis 6 ga watan Afrilu, 2023 a sakatariya ta ƙasa
- Wani tsagin mambobin kwamitin gudanarwa NWC sun ware kansu sun naɗa shugaban jam'iyya na rikon kwarya
- Sun ɗauki wannan matakin ne sakamakon zaman da suka yi bayan umarnin babbar kotun birnin tarayya Abuja
Abuja - Wasu mutane da ake zargin 'yan daban siyasa ne sun kutsa kai cikin Hedkwatar jam'iyyar Labour Party da ke babban birnin tarayya Abuja.
Shugaban Labour Party na ƙasa, Julius Abure, shi ne ya bayyana haka a wata sanarwa da ya fiyar ranar Alhamis 6 ga watan Afrilu, 2023.
A cewar Mista Abure, mutanen da ake tsammanin 'yan daban siyasan ne sun kutsa ta tsiya-tsiya suka shiga Hedkwatar LP ta ƙasa, kamar yadda Vanguard ya rahoto.
Mataimakin Shugaban APC Ya Fasa Kwai Kan Yadda Ake Bayar Da Cin Hanci Don Samun Shugabancin Majalisa
Babbar Sakatariyar LP ta ƙasa na a Anguwar Utako kusa da ofishin ƙungiyar 'yan jarida (NUJ) da ke babban birnin tarayya.
DUBA: Shigo shafin Legit.ng na manhajar Legit.ng na Telegram! Kada ka bari komai ya wuce ka
Wane mutane ne suka shiga Sakatariyar?
Wani rahoto na daban ya yi ikirarin cewa waɗanda suka shiga cikin Sakatariyar ba wasu bane illa mambobin kwamitin gudanarwa na LP ta ƙasa su Bakwai.
Tawagar jiga-jigan sun ware kansu, sun naɗa mataimakin shugaban jam'iyya na shiyyar kudu, Lamidi Bashir Apapa, a matsayin muƙaddashin jam'iyya.
Tawagar mambobin NWC ɗin guda bakwai bisa rakiyar wasu jami'an 'yan sanda ne suka kutsa cikin Sakaatariyar ranar Alhamis.
Da yake jawabi, Apapa ya ce wannan naɗin ya samo asali ne daga taron gaggawan da NWC ta gudanar kan hukuncin da babbar Kotun birnin tarayya ta yanke.
Kotun ta umarci Julius Abure ya dakatar da ayyana kansa a matsayin shugaban LP na ƙasa tare da Sakatarensa da wasu shugabanni biyu duk kan amfani da takardun bogi.
El-Rufai Ya Yaba Wa Gwamna Wike
A wani labarin kuma El-Rufai Ya Yaba Wa Gwamna Wike, Yace Mutanen Ribas Sun Yi Abinda Ya Dace
Gwamna Malam Nasiru El-Rufai na jihar Kaduna ya ziyarci jihar Ribas domin kaddamar da aikin da takwaransa, gwamna Wike ya zuba wa talakawan jiharsa.
El-Rufai ya ce a karon farko PDP ta gaza samun tanadin kwansutushin na kaso 25 cikin 100 tun shekarar 1999.
Asali: Legit.ng