El-Rufai Ya Yaba Wa Gwamna Wike, Yace Mutanen Ribas Sun Yi Abinda Ya Dace
- Gwamnan Kaduna, Malam Nasiru El-Rufai, ya yaba wa takwaransa na jihar Ribas, Nyesom Wike, bisa tsayawa kai da fata mulki ya koma kudu
- El-Rufai ya amsa gayyatar Wike na zuwa Ribas da kaddamar da ɗaya daga cikin ayyukansa ranar Alhamis
- Ya ce mutanen Ribas sun kafa tarihi a zaɓen shugaban kasa kuma sun nuna waye wa a siyasa
Rivers - Gwamna Malam Nasiru El-Rufa'i na jihar Kaduna ya yaba wa takwaransa na jihar Ribas, Nyesom Wike, bisa goyon bayan mulkin Najeriya ya koma kudu a zaɓen 2023.
Malam El-Rufai ya yaba wa Wike ne yayin kaddamar Titunan da suka haɗa Eneka-Igbo Etche, a ƙaramar hukumar Obio-Akpo, jihar Ribas ranar Alhamis.
Ya ce mazauna jihar mai ɗumbin albarkatun man Fetur a shiyyar kudu maso kudancin Najeriya sun zaɓi, "Nagarta a saman jam'iyyar da suke ƙauna a zuciya."
Channels tv ta rahoto gwamna El-Rufai na cewa:
DUBA: Shigo shafin Legit.ng na manhajar Legit.ng na Telegram! Kada ka bari komai ya wuce ka
"A madadin ɗan takarar shugaban kasa na jam'iyyarmu, ina mai gode maka (Wike) da ɗaukacin mazauna Ribas bisa ɗaukar hanya mai ɓullewa na zaɓen Asiwaju Bola Ahmed Tinubu."
"A karon farko tun bayan fara Jamhuriya ta huɗu a 1999, PDP ta gaza samun kaso 25% na kuri'un jihar Ribas. Wannan ya nuna mutanen Ribas suna iya tantance aya da tsakuwa."
"Sun san lokacin da ya dace su yi karatun ta natsu su zabi nagarta kuma sun zaɓi wanda ya dace fiye da son zuciyarsu a siyasa. Muna gode maka bisa samar da irin wannan shugabancin, gwamna Wike."
Wike, jigon jam'iyyar PDP ya fito fili ya nuna adawarsa da takarar Atiku Abubakar, ya ce ya kamata a yi adalci ta hanyar baiwa kudu mulki bayan Buhari ya gama shekara 8.
Yayin haka ne gwamna Wike ya haɗa karfi da wasu takwarorinsa gwamnonin PDP suka kafa tawagar G-5 wacce ta kunshi, Wike, Okezie Ikpeazu (Abia), Ifeanyi Ugwuanyi (Enugu), Samuel Ortom (Benue) da Seyi Makinde (Oyo).
A zaɓen shugaban kasa, Atiku ya sha kashi a baki ɗaya jihohin gwamnonin G-5, Peter Obi ya lashe Abiya da Enugu, Tinubu ya ci Benuwai, Oyo da Ribas, kamar yadda Vanguard ta ruwaito.
Mun koya wa Ganduje darasin siyasa tsawon rayuwarsa, Jibrin
A wani labarin kuma Makusancin Kwankwaso ya bayyana yadda suka koya wa Ganduje darasin siyasa a zaɓen jihar Kano
Zabaɓɓen ɗan majalisar tarayya, Abdulmumini Jibrin, ya ce gwamna Abdullahi Ganduje ne ya fusata su a jam'iyyar APC ya tilasta musu sauya sheƙa zuwa NNPP.
Asali: Legit.ng