Ndume Ya Shiga Cikin Masu Neman Kujerar Shugabancin Majalisa, Ya Lissafa Manufofinsa 10
- Mohammad Ndume ya bi sahun masu neman shugabancin majalisar dattawa a zango na 10 na majalisar
- Ndume ya kasance na farko da ya fitar da manufofin tsayawa takarar shugabancin majalisar
- Cikin manufofi 10 da ya fitar, Ndume ya ce zai fifita bukatun Najeriya da yan Najeriya idan ya zama shugaban majalisar
Tsohon shugaban masu rinjaye kuma sanata mai wakiltar Borno ta Arewa, Mohammed Ali Ndume, ya bayyana kudirinsa na neman shugabancin majalisar dattawa a zango na 10 na majalisar.
Ndume ya kuma fitar da manufofi 10 da zai aiwatar in ya zama shugaban majalisar dattawan, The Nation ta rahoto.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Ndume ne na farko da ya fitar da manufofin neman shugabancin majalisar cikin jerin ma su neman takarar
Leadership ta ruwaito Ndume ya tsaya takarar a 2019 amma ya sha kaye a hannun shugaban majalisar dattawa mai ci, Ahmad Lawan.
Ya bukaci yan Najeriya musamman yan jam'iyyarsa da su bari sanatocin su zabi shugaban saboda muhimmancin kujerar.
A ra'ayin Ndume, a matsayinsa na gogaggen sanata, ya kamata ya tsaya takarar, ya kuma ce ragowar sanatocin za su yanke wanda zai jagorance su.
Manufofi 10 Da Sanata Ndume ya fitar
A manfofi 10 da ya fitar wanda jaridar Leadership ta samo, Ndume ya ce zai fifita bukatar Najeriya da yan Najeriya.
Kamar yadda Ndume ya rubuta:
Shugaban majalisar dattawa kamar kowa ne. Zai yi aiki kafada da kafada da bangaren zartarwa da na shari'a ba tare da shiga aikin kowa ba; kirkira da kuma sabunta dokoki don yin daidai da bukatun yan Najeriya.
- Tsaro da walwalar yan kasa
- Samar da aikin yi
- Cigaban tattalin arziki
- Yaki da rashawa
- Ilimi
- Damawa a siyasa
- Habbaka kasuwanci da kananan sana'o'i
- Habbaka kiwon lafiya
- Bibiya da kuma gyara dokar haraji ta yadda
- Karewa tare da inganta walwalar ma'aikatan majalisar
Orji Kalu: Lokacin Da Zan Zama Shugaban Majalisar Dattawa Ya Yi
A wani rahoton mai alaka da wannan, Sanata Orji Kalu, babban mai tsawatarwa na majalisar dattawan Najeriya ya sanar da niyyarsa na shiga takarar shugabancin majalisar tarayya zubi na 10.
Kalu wanda ke wakiltar mazabar Abia ta Arewa a majalisar, ya furta hakan ne a ranar Talata lokacin da ya ke zantawa da manema labarai a majalisar.
Asali: Legit.ng