Wata Kungiya Ta Bayyana Wanda Ya Cancanci Matsayin SGF a Gwamnatin Tinubu, Ta Bayar Da Dalilanta

Wata Kungiya Ta Bayyana Wanda Ya Cancanci Matsayin SGF a Gwamnatin Tinubu, Ta Bayar Da Dalilanta

  • Wata ƙungiya ta fara kiran Tinubu ya ba gwamnan jihar Plateau muƙamin sakataren gwamnatin tarayya a gwamnatin sa
  • Ƙungiyar tace Simon Lalong ya cancanci samun wannan kujerar domin saka masa wahalar da yiwa APC
  • Ƙungiyar ta kuma yi bayani kan dalilan da ya sanya take kiran Tinubu ya ba Lalong SGF a gwamnatin sa

Jos, Plateau- Jagororin jam'iyyar All Progressives Congress (APC) a ƙarƙashin ƙungiyar North Central APC Forum, sun yi kira ga zaɓaɓɓen shugaban ƙasa Bola Tinubu, da ya zaɓi Simon Lalong a matsayin sakataren gwamnatin tarayya a gwamnatin sa. Rahoton Daily Trust

A cewar ƙungiyar, ba Simon Lalong muƙamin na SGF zai kuma tabbatar da cewa anyi adalci a cikin gwamnati mai zuwa ta yadda kowane ɓangare zai yi na'am ya san ana damawa da shi. Rahoton Independent

Kara karanta wannan

Ba Bashi: Ministan Buhari Ya Bayyana Wani Muhimmin Alkawari Da Shugaba Buhari Ya Cikawa 'Yan Najeriya

Lalong
Wata Kungiya Ta Bayyana Wanda Ya Cancanci Matsayin SGF a Gwamnatin Tinubu, Ta Bayar Da Dalilanta Hoto: Daily Trust
Asali: UGC

Da yake jawabi a madadin ƙungiyar a birnin Jos bayan sun gudanar da taron gaggawa, shugaban ƙungiyar Alhaji Saleh Mandung Zazzaga, yace Lalong ya wahaltawa APC, Arewacin Najeriya, a matsayin sa na shugaban gwamnonin Arewacin Najeriya, jihar Plateau da zaman Tinubu shugaban ƙasa.

A kalamansa:

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

“Gwamna Simon Lalong yayi sadaukarwa sosai ga APC, Arewacin Najeriya, ƙasa gabaɗaya. Mutum ne mai son zaman lafiya wanda ya samu nasarori da dama kuma shugaba ne wanda baya nuna wariya. Wani abin burgewa dangane da shi shine rawar da ya taka a zaɓen shugaban ƙasa na APC."
"Ƙungiyar mu da sauran ƙungiyoyi da wasu manyan mutane mun yi kiran da a bashi takarar shugaban ƙasa daga yankin Arewa ta Tsakiya saboda gudunmawar da yankin ya bayar, Amma ba muyi nasara ba, sai muka koma neman a bashi mataimakin shugaban ƙasa tun da an amince a miƙa mulki zuwa yankin Kudu"

Kara karanta wannan

Gaskiya Ta Bayyana, Dan Takarar Gwamnan APC Ya Tono Kulla-Kullar Da Ake Shirya Masa Don Hana Shi Zuwa Kotu

"Saboda haka ƙoƙarin da Lalong yayi ya sanya yakamata a bashi matsayin SGF. Ba wai kawai ya dace da kujerar bane, amma ya cancanta kuma zai kawo ƙwarewar sa wajen shugabanci domin ciyar da ƙasar nan gaba."

Sanatan APC Ya Yi Kus-Kus da Buhari a Aso Villa, Ya ce Zai Zama Shugaban Majalisa

A wani labarin na daban kuma, sanatan APC ya sanya labule da shugaban ƙasa Muhammadu Buhari, yace kujerar shugaban majalisar dattawa tasa ce.

Sanata Osita Isunazo ya bayyana dalilan da suka sanya yakamata ya ɗare shugabancin majalisar.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sharif Lawal avatar

Sharif Lawal Sharif Lawal ma'aikacin jarida ne wanda ya samu gogewa a harkar aikin jarida. Ya yi digirinsa na farko a jami'ar Ahmadu Bello (ABU) da ke Zaria. Ya samu horo daga Reuters kan aikin jarida da tantance labarai. Za a iya tuntubarsa ta Sharif.lawal@corp.legit.ng