2023: Wike Ya Yaba Wa Gwamna Ortom Bisa Goyon Bayan Mulkin Ya Koma Kudu

2023: Wike Ya Yaba Wa Gwamna Ortom Bisa Goyon Bayan Mulkin Ya Koma Kudu

  • Gwamna Nyesom Wike na jihar Ribas ya yaba wa takwaransa na jihar Benuwai dake arewa ta tsakiya, Samuel Ortom
  • Ya ce mai yuwuwa ana ganin Ortom ya sha kashi a zaben gwamna da Sanata amma ba haka lamarin yake ba
  • Wike ya gode wa Ortom bisa jajircewa kan wajibi mulki ya koma kudancin Najeriya bayan shekaru 8 ɗin Buhari

Rivers - Gwamnan jihar Ribas, Nyesom Wike, ya yaba wa takwaransa na jihar Benuwai, Samuel Ortom, bisa goyon bayan mulkin ƙasa ya koma kudancin Najeriya.

Wike ya yi wannan magana ne a wurin kaddamar da makarantar Sakandiren gwamnati a Kpor, ƙaramar hukumar Gokana, jihar Ribas, kamar yadda Channels ta rahoto.

Gwamna Wike da Samuel Ortom.
2023: Wike Ya Yaba Wa Gwamna Ortom Bisa Goyon Bayan Mulkin Ya Koma Kudu Hoto: channelstv
Asali: UGC

Ortom na ɗaya daga cikin gwamnonin da suka ware a PDP suka kafa tawagar G-5, a lokacin kakar zaɓen 2023 kuma suka nemi mulki ya koma kudu daga arewa.

Kara karanta wannan

Babbar Magana: Gwamna Wike Bai Hakura Ba, Ya Kara Dauko Hanyar Ruguza Jam'iyyar PDP

Gababin zaɓen watan Fabraairu, Gwamna Ortom ya ayyana goyon bayansa ga Peter Obi bayan raba gari da Atiku Abubakar. Ya nemi takarar Sanata amma APC ta lallasa shi.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Wike ya jinjina wa Ortom

Da yake jawabi ranar Talata, Wike ya ce gwamna Ortom ne haƙiƙanin wanda ya samu nasara a babban zaɓen da aka kammala duk da kashin da ya sha a zaɓen gwamna da Sanata.

Gwamnan ya kuma gode wa Ortom bisa goyon bayan mulki ya koma kudu, wanda a ganinsa wannan ne ya sa wasu masu adawa suka masa taron dangi.

Da yake ayyana Ortom a matsayin ɗan uwansa, Wike ya ce tarihi ba zai manta da shi ba kuma ya tabbatar masa da cewa jama'ar jihar Ribas zasu tsaya masa a ko wane lokaci.

Da yake magana ga Ortom, gwamnan Ribas ya ce:

Kara karanta wannan

Fadar Shugaban Kasa Ta Tabbatar da Murabus Ɗin Wani Ministan Buhari, Ta Fallasa Sunansa

"Mai yuwuwa kana tunanin ka karɓi aya a hannu, ba haka bane kaine sahihin wanda ya samu nasara. Ina gode maka bisa tsaya kan mulki ya koma kudu, ka samu tasgaru kan haka amma tarihi ba zai manta da kai ba."

Ribas Zata Goyi Bayan Wanda APC Ke So Ya Zama Kakakin Majalisar Wakilai, Wike

A wani labarin kuma Gwamna Wike ya kara kawo cikas a cikin jam'iyyar PDP, ya ce jiharsa na tare da APC a matakin ƙasa

Gwamnan ya ce yan majalisun tarayya daga Ribas zasu marawa duk wanda shugabannin APC suka zabi ya zama kakakin majalisar wakilai.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262