Yaron Ganduje Ya Garzaya Kotu Domin Kalubalantar Kashin Da Ya Sha a Zabe
- Yaron gwamnan jihar Kano, Abdullahi Umar Ganduje, ya garzaya kotu domin ƙalubalantar kayen da yasha a zaɓe
- Umar Abdu Umar na ƙalubalantar nasarar da ɗan takarar NNPP, Tijjani Abdulkadir Jobe, yayi a kansa.
- Umar ya sha kashi ne dai a zaɓen kujerar ɗan majalisar wakilai ta Rimin Gado, Dawakin-Tofa da Tofa
Jihar Kano- Umar Abdu Umar yaron gwamnan Kano, Abdullahi Umar Ganduje, ya kai ƙara gaban kotun sauraren ƙararrakin zaɓe domin ƙalubalantar kayen da ya sha a zaɓen ɗan majalisar tarayya.
Umar wanda yayi takarar kujerar majalisar tarayya a ƙarƙashin inuwar jam'iyyar All Progressives Congress (APC) da Tijjani Abdulkadir Jobe, na jam'iyyar New Nigeria Peoples Party (NNPP), ya ƙi amincewa da sakamakon zaɓen. Rahoton Daily Trust.
Hukumar zaɓe mai zaman kanta ta ƙasa (INEC) a jihar Kano, ta bayyana Abdulkadir Jobe a matsayin wanda ya lashe zaɓen kujerar ɗan majalisar tarayya mai wakiltar Rimin Gado, Dawakin Tofa ɗa Tofa a majalisar wakilai ta tarayya.
Gaskiya Ta Bayyana, Dan Takarar Gwamnan APC Ya Tono Kulla-Kullar Da Ake Shirya Masa Don Hana Shi Zuwa Kotu
Umar, ta hannun lauyan sa, Barista A.T Falola, yana kuma ƙalubalantar hukumar INEC na bayyana Jobe a matsayin ɗan takarar da ya samu mafi yawan a ƙuri'u a lokacin da aka gudanar da zaɓen.
Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!
Lauyan na sa, Falola ya nemi kotun sauraron ƙararrakin da ta bari a ba Jobe da jam'iyyar sa ta NNPP ƙarar da yake yi musu. Rahoton Allnews
Kotun sauraron ƙarar ta amince da buƙatar da yaje da ita a gabanta.
Umar Abdu Umar ya samu nasarar kayar da Jobe wanda shine ɗan majalisa mai ci yanzu na yankin Rimin Gado, Dawakin-Tofa da Tofa a majalisar wakilai ta tarayya, a zaɓen fidda gwani na jam'iyyar APC.
Bayan shan kayen da yayi a hannun Umar, sai Jobe ya tattara komatsansa ya fice daga jam'iyyar APC, sannan ya koma jam'iyyar NNPP inda ya samu tikitin takara.
Wasu Matasa Sun Kunno Wuta Suna Neman a Soke Zaban Sanata Mace a Abuja
A wani labarin na daban kuma, wasu matasa na neman hukumar zaɓe ta ƙasa (INEC) ta soke zaɓen sanatan birnin tarayya Abuja.
Matasan na neman hukumar zaɓen da ta sake sabon zaɓe a kujerar sanatan na birnin tarayya Abuja, wacce Ireti Kingibe, ta samu nasarar lashewa.
Asali: Legit.ng