Jam'iyyar APC Ta Dakatar Da Wasu Manyan Jiga-Jiganta a Jihar Edo

Jam'iyyar APC Ta Dakatar Da Wasu Manyan Jiga-Jiganta a Jihar Edo

  • Rigima ta kunno kai a jam'iyyar APC reshen ƙaramar hukumar Uhunmwode dake jihar Edo
  • Kwamitin zartarwar jam'iyyar na ƙaramar hukumar ya dakatar da wasu jiga-jigan jam'iyyar na ƙaramar hukumar
  • Kwamitin dai yana yi musu tarin zarge-zarge waɗanda suka sanya ya dakatar da su har sai an kammala bincike

Jihar Edo- Jam'iyyar All Progressives Congress (APC) ta dakatar da tsohon ɗan majalisar tarayya, Simon Osagie, da wasu mutum goma bisa zargin yi mata zagon ƙasa.

Dakatarwar ta su ta biyo ne ta hannun ƴan kwamitin zartarwar jam'iyyar APC na ƙaramar hukumar Uhunmwode ta jihar Edo a ƙarƙashin jagorancin Osawe Osayemwenre. Rahoton Punch

Sauran da aka dakatar ɗin sun haɗa da Rolland Alari, Felix Alari, Simon Uduogie, Mrs. Esohe Idemudia, Monday Guobadia, Nelson Gomez Ise, Festus Iyekeoretin, Jolly lyekeoretin, Evans Ozabor da William Amadi. Rahoton Tribune

Kara karanta wannan

Wasu Matasa Sun Kunno Wuta Suna Neman a Soke Zaban Sanata Mace a Najeriya

Simon Osagie
Jam'iyyar APC Ta Dakatar Da Wasu Manyan Jiga-Jiganta a Jihar Edo Hoto: Twitter/@samsonosagie5
Asali: Twitter

Dakatarwar ta su na ƙunshe ne a cikin wata takarda da aka aikewa shugaban jam'iyyar na jihar Col. David Imuse, (retd.), mai taken “Sanarwar dakatar da Hon. Samson R. Osagie, Hon. Roland Alari da sauran su"

DUBA: Bibiyemu a Instagram don samun labarai masu muhimmanci kai tsaye cikin manhajar

Takardar wacce Osayemwenre da sauran mambobi 17 suka rattaɓawa hannu na cewa:

"Bayan tarin ƙorafe-ƙorafen yiwa jam'iyya zagon ƙasa, ƙirƙirar ɓangare, rashin halartar taron jam'iyya da ɓarna da gangan a manyan zaɓukan da aka kammala, daga wajen wasu jiga-jigan jam'iyya, mu na sanar da dakatar da waɗannan mutanen daga reshen jam'iyyar APC na Uhunmwode LGA."
“Muna roƙon ka da kayi amfani da matsayin ka wajen tabbatar da wannan dakatarwar domin hana su yi mana katsalandan a binciken da za a gudanar."
"Mun kafa kwamitin ladabtarwa mai mutum uku a ƙarƙashin jagorancin Farfesa David Osifo, Dr. Washington Osifo a matsayin sakatare da Dan Ogbegie, a matsayin mamba."

Kara karanta wannan

Jam'iyya Ta Bi Sahun PDP, Ta Dakatar da Shugabanta Na Ƙasa Kan Muhimmin Abu, Rigima Ta Kaure

APC ta Bude Kofar Rikici da Korar Mataimakin Shugaban Majalisa da Tsohuwar Hadimar Buhari

A wani labarin na daban kuma, jam'iyyar APC a jihar Delta ta dakatar da.ɗan takarar gwamnan ta kuma mataimakin shugaban majalisar dattawa mai ci yanzu.

Jam'iyyar tace ta dakatar da sanata Omo-Ovie Agege ne bisa tulin wasu laifuka.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sharif Lawal avatar

Sharif Lawal Sharif Lawal ma'aikacin jarida ne wanda ya samu gogewa a harkar aikin jarida. Ya yi digirinsa na farko a jami'ar Ahmadu Bello (ABU) da ke Zaria. Ya samu horo daga Reuters kan aikin jarida da tantance labarai. Za a iya tuntubarsa ta Sharif.lawal@corp.legit.ng