Majalisa Ta 10: Mai Neman Shugabancin Majalisa Ya Samu Tagomashi, Wani Babban Gwamna Ya Mara Masa Baya
- Gwamnan jihar Nasarawa, Abdullahi Sule, ya nuna goyon bayan sa kan neman shugabancin majalisar Wakilai da Idris Waje yake yi
- Gwamnan yace shi da kansa zai jagoranci kamfen ɗin Wase domin ganin ya samu shugabancin majalisar
- Gwamna Sule ya lissafo wasu halaye na ɗan majalisar waɗanda suka sanya ya cancanta ya samu shugabancin majalisar
Jihar Nasarawa- Gwamnan jihar Nasarawa, Abdullahi Sule, ya nemi da ya jagorancin kamfen ɗin mataimakin shugaban majalisar wakilai, Ahmed Idris Wase, na zama kakakin majalisar wakilai ta goma. Rahoton Leadership
Gwamna Sule ya gayawa Wase wanda ya jagoranci wasu ƴan majalisu 15 zuwa gidan gwamnan a Abuja, cewa batun shugabancin majalisar wakilan ta goma kamata yayi ya kasance akan cancanta ne ba wani abu daban ba.
“Ba kawai ina goyon bayan yankin Arewa na tsakiya ya samu shugabancin bane, ina goyon bayan ka domin zama kakakin majalisar wakilai na gaba. Zan kasance a gaba-gaba wajen jagorantar kamfen ɗin ka." Inji gwamnan
Gwamna Sule yayi nuni da cewa bayan ƙwarewar da Wase yake da ita, juriyar sa wajen cimma abinda ya sanya a gaba da ƙanƙan da kansa ya sanya ya kerewa sauran masu neman shugabancin majalisar. Rahoton Vanguard
DUBA: Shigo shafin Legit.ng na manhajar Legit.ng na Telegram! Kada ka bari komai ya wuce ka
A kalamansa:
"Tabbas muna sane cewa maganar shugaban majalisa ta gaba an fara yin ta duk da ba a hukumance ba. Ni a karan kai na baka bukatar zuwa ka sanar da ni saboda ni da kai na zan jagoranci kamfen ɗin ka na zama kakakin majalisa domin yankin Arewa ta tsakiya ya samu kujerar."
“Idan za ayi amfani da shawarata, maganar shugabancin majalisa kan ƙwarewa da cancanta za ayi ta. Dukkanin guda biyu kana da su. Ni da mutanen jihar Nasarawa muna goyon bayan ka."
Wase tunda farko ya gayawa gwamnan cewa yankin Arewa ta Tsakiya ya cancanci ya amfana sosai da gwamnatin gaba mai zuwa.
Duk Da NNPP Ta Yi Nasara A Kano Kwankwaso Ya Zargi Buhari Kan Rashin Shirya Zaben Gaskiya
A wani labarin na daban kuma, madugun kwankwasiyya ya zargi shugaba Buhari da rashin shirya sahihin zaɓe a ƙasar nan.
Rabiu Musa Kwankwaso yayi takarar shugaban ƙasa a ƙarƙashin inuwar jam'iyyar NNPP amma bai samu nasara ba.
Asali: Legit.ng