Kiristan Kudu Ne Ya Kamata Ya Zama Shugaban Majalisar Dattawa, In ji Dan Majalisa
- Mamba mai wakiltan mazabar Egbeda/Ona Ara ta jihar Oyo a majalisar wakilai, Akin Alabi, ya magantu kan wanda ya cancanci zama shugaban majalisar dattawa
- Alabi ya ce wani kirista daga kudu maso gabas ko kudu maso kudu ne ya kamata ya zama shugaban majalisar dattawa na gaba
- Ya ce hakan shine adalci kasancewar Bola Tinubu, zababben shugaban kasa da mataimakinsa, Kashim Shettima duk Musulmai ne
Gabannin rantsar da majalisar dokokin tarayya ta 10 a watan Yuni, dan majalisa mai wakiltan mazabar Egbeda/Ona Ara ta jihar Oyo, Akin Alabi ya taya kiristan kudu zawarcin kujerar shugaban majalisar dattawa, Channels TV ta rahoto.
Tuni dai wasu zababbun sanatoci suka nuna ra'ayinsu a kan wannan kujera. Sun hada da Orji Uzor Kalu, Jibrin Barau, Sani Musa, Godswill Akpabio, Dave Umahi, Osita Izunaso da Ahmad Lawan.
Orji Kalu Ya Fadi Abun da Zai Yi Idan Tinubu Ya Nemi Ya Ajiye Kudirinsa Na Son Zama Shugaban Majalisar Dattawa
Koda dai jam'iyyar All Progressives Congress (APC) bata rigada ta raba mukaman zuwa yanki ba, Alabi na sa ran cewa kamata ya yi ace shugaban majalisar dattawa na gaba ya kasance dan kudu.
Da yake magana a shirin Channels TV na Politics Today, Alabi ya bayyana cewa tun da zababben shugaban kasa, Bola Tinubu da mataimakinsa, Kashim Shettima sun kasance Musulmai, zai zama daidai ne Kirista ya shugabanci majalisar tarayyar.
DUBA: Shigo shafin Legit.ng na manhajar Legit.ng na Telegram! Kada ka bari komai ya wuce ka
Alabi ya ce:
"Mun fahimci cewa lokacin da zababben shugaban kasa ke zabar abokin takararsa, ana ta duba abubuwa kamar shi Musulmi ne. Addinin Musulunci shine mara rinjaye a kudu. Idan ya zabi kirista a matsayin abokin takara, wannan zai zama mara rinjaye daga kudu.
"Don haka, zai iya zama ba tikiti mai karfi ba, don haka muka je ma Musulmi da Musulmi. Wannan ya rigada ya fitar da manyan mutane daga arewa maso yamma saboda su Musulmai ne.
"Idan za mu yada shi, ya zama dole ya tafi bangaren kudu - kiristan kudu. Ba kudu maso yamma ba kamar yadda na fadi, zai kasance kudu maso gabas ko kudu maso kudu."
Zan janye daga tseren shugabancin majalisar dattawa idan Tinubu ya bukaci haka, Kalu
A wani labarin kuma, Sanata Orji Uzor Kalu, shugaban masu tsawatarwa a majalisar dattawa ya bayyana cewa a shirye yake ya janye daga tseren shugabancin majalisar dattawa idan har zababben shugaban kasa, Bola Tinubu ya bukaci haka.
Asali: Legit.ng