Boss Mustapha: Buhari Ba Zai Kara Ko Kwana Daya Ba a Mulki

Boss Mustapha: Buhari Ba Zai Kara Ko Kwana Daya Ba a Mulki

  • Sakataren gwamnatin tarayya, Boss Mustapha ya magantu kan yadda tsarin mika mulki ga gwamnati na gaba zai kasance
  • Mustapha ya ce Shugaban kasa Muhammadu Buhari ba zai kara ko kwana daba ba a mulki daga ranar 29 ga watan Mayu
  • Ya ce tuni shirye-shiryen mika mulki suka kankama don ganin an yi shi cikin lumana kuma a hukumance kamar yadda kundin tsarin mulki ya tanada

Abuja - Babban sakataren gwamnatin tarayya, Boss Mustapha, ya ce Shugaban kasa Muhammadu Buhari ba zai kara ko kwana daya ba a kan mulki.

Bayan kammala zaben shugaban kasa a watan Fabrairu, ana sanya ran Buhari zai mika mulki ga zababben shugaban kasa, Bola Tinubu a ranar 29 ga watan Mayu.

Zababben shugaban kasa, Bola Tinubu tare da Shugaba Muhammadu Buhari
Boss Mustapha: Buhari Ba Zai Kara Ko Kwana Daya Ba a Mulki Hoto: Femi Adesina
Asali: Facebook

Buhari zai mika mulki ga Bola Tinubu a ranar 29 ga watan Mayu, Boss Mustapha

Kara karanta wannan

Babban Abinda Yasa Yan Najeriya Za Su Yi Kewar Buhari Su Ji Kamar Ya Dawo Bayan Ya Sauka Daga Mulki

Da yake jawabi ga taron manema labarai a Abuja a ranar Talata, Mustapha, shugaban kwamitin mika mulki na shugaban kasa, ya ce ana nan ana ta kokari don ganin ba a samu tangarda ba wajen mika mulki, rahoton The Cable.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Channels TV ta nakalto Mustapha yana cewa:

"Batu ne na kundin tsarin mulki kuma koda an warware kararrakin da suka shafi zabe ko ba a warware ba, ba zai hana mika mulki ba a ranar 29 ga watan Mayu.
"Shugaban kasa Muhammadu Buhari ba zai kara ko kwana daya ba bayan 29 ga watan Mayu wajen mika mulki ga duk wanda INEC ta ayyana ba.
"Za a ci gaba da zaman kotu kuma muna yin duk mai yiwuwa don tabbatar da cewar ba a samu tangarda ba a tsarin mika mulkin; gwamnatin tarayya ta saki jawabi a kan haka.

Kara karanta wannan

Karin bayani: INEC ta fadi ranar da za a karasa zaben da ba a kammala ba a Najeriya

"Tsarin mika mulkin na kan hanya kuma ana kokarin ganin an yi shi cikin nasara kuma a ranar 29 ga watan Mayu, za a mika mulki ga sabon zababben shugaban kasa cikin lumana a hukumance."

Tinubu ya mika sunayen mambobin kwamitin karbar shugabanci

A wani labarin kuma, mun jin cewa zababben shugaban kasa, Asiwaju Bola Tinubu ya mika sunayen gwamnan jihar Kebbi, Sanata Atiku Bagudu da tsohon kwamishinan jihar Lagas, Cif Olawale Edun a matsayin mambobin kwamitin karbar mulki na PTC.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Musa avatar

Aisha Musa (Hausa writer) Aisha Musa 'yar jarida ce wacce ta kwashe shekaru biyar tana aikin gogewa a harkar yada labarai. Ta kammala karatun ta a Jami'ar Ibrahim Badamasi Babangida (IBB Lapai) a shekarar 2014 tare da digirin farko a fannin Tarihi. Aisha Editan Hausa ce wacce ke amfani da kwarewa da kwazonta don karfafawa wasu gwiwar yin aiki tukuru don cimma nasara. Ta karbi lambar yabo na gwarzuwar shekarar 2021 a bangaren Hausa na Legit. Za ku iya aika mata sakonnin imel ta adireshinta aisha.musa@corp.legit.ng