Dan Takarar Gwamnan PDP Na Jihar Cross Rivers, Yayi Watsi Da Sakamakon Zaben Gwamnan Jihar

Dan Takarar Gwamnan PDP Na Jihar Cross Rivers, Yayi Watsi Da Sakamakon Zaben Gwamnan Jihar

  • Ɗan takarar gwamnan jihar Cross Rivers a ƙarƙashin jam'iyyar PDP ya shirya ƙalubalantar sakamakon zaɓen gwamnan jihar
  • Ɗan takarar ya bayyana cewa an tafka kura-kurai a zaɓen wanda hakan ya sanya zai garzaya kotu
  • Ya kuma roƙi magoya bayan sa da su kwantar da hankulan su inda ya basu tabbacin kotu zata yi musu adalci

Jihar Cross Rivers - Ɗan takarar gwamnan jihar Cross Rivers a ƙarƙashin inuwar jam'iyyar Peoples Democratic Party(PDP), Farfesa Sandy Ojang Onor, ya sha alwashin ƙalubalantar sakamakon zaɓen gwamnan jihar.

Ɗan takarar gwamnan ya bayyana zaɓen gwamnan da aka gudanar a jihar a matsayin wanda yake cike da kura-kurai. Rahoton Vanguard

Sandy
Dan Takarar Gwamnan PDP Na Jihar Cross Rivers, Yayi Watsi Da Sakamakon Zaben Gwamnan Jihar Hoto: Ripples Nigeria
Asali: UGC

Bayan ɗan takarar ya kammala tattaunawa tsakanin sa da lauyoyin sa, masu ruwa da tsaki kan yadda aka gudanar da zaɓen, ya yanke shawarar garzayawa kotu domin kai koken sa. Rahoton Tribune

Kara karanta wannan

APC Vs PDP: Tashin Hankali Yayin Da Kotun Daukaka Kara Zata Yanke Hukunci Yau Kan Sahihin Gwamnan Jihar Osun

A wata sanarwar da Onor ya rattaɓawa hannu, yace zaɓen akwai kura-kura sosai a cikin sa da suka haɗa da siyan ƙuri'u, maguɗin zaɓe, barazana da dai sauran su.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Ya bayyana cewa jami'an hukumar zaɓe mai zaman kanta ta ƙasa (INEC), tare da taimakon jami'an tsaro sun tafka maguɗi inda suka sauya sakamakon zaɓen.

“A kowane irin zaɓe ya kan ginu ne akan turbar samun wanda yayi nasara da wands ya samu akasin ta, amma dole ne ya kasance ta hanya sahihiya." Inji shi
Mun tattauna da lauyoyin mu, masu ruwa da tsaki domin yin duba ga yadda aka gudanar da zaɓen. Daga ƙarshe mun cimma matsaya cewa dole ne mu ƙalubalance shi a gaban kotu."
“Mun yi hakan ne domin cimma burin da mafiya yawan al'umma Cross Rivers suke da shi. Muna da ƙwarin guiwar cewa za mu samu adalci."

Kara karanta wannan

Yan Jagaliya Sun Kaddamar da Hari a Ofishin APC dake Zamfara, Biyu Sun Tafi Lahira

Ɗan takarar ya kuma yi kira ga magoya bayan sa da su kwantar da hankalin su, yayin da suke ƙoƙarin ƙwato haƙƙin su a gaban kotu.

Gwamna Wike Ya Bayyana Abinda Zai Yi Bayan Ya Sauka Daga Mulki

A wani labarin na daban kuma, gwamnan jihar Rivers ya bayyana abinda zai yi idan wa'adin mulkin na gwamna ya cika.

Gwamnan ya kuma yi ƙarin haske kan yiwuwar hukumar EFCC ta cafke shi.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sharif Lawal avatar

Sharif Lawal Sharif Lawal ma'aikacin jarida ne wanda ya samu gogewa a harkar aikin jarida. Ya yi digirinsa na farko a jami'ar Ahmadu Bello (ABU) da ke Zaria. Ya samu horo daga Reuters kan aikin jarida da tantance labarai. Za a iya tuntubarsa ta Sharif.lawal@corp.legit.ng