Yanzu Yanzu: PDP Ta Dakatar Da Iyorchia Ayu Saboda Cin Dunduniyar Jam’iyya
- Shugabannin kwamitin gudanarwa na PDP a gudunmar Igyorov ta karamar hukumar Gboko sun dakatar da shugaban jam'iyyar na kasa, Iyorchia Ayu
- An dakatar da Ayu ne kan zarginsa da yi wa jam'iyyar zagon kasa wanda ya kai ga faduwarta a zaben jihar
- Shugabannin jam'iyyar sun kuma zargi Ayu da kin kada kuri'a a zaben ranar 18 ga watan Maris
Benue - Rahotanni sun kawo cewa an dakatar da Iyorchia Ayu, shugaban jam'iyyar Peoples Democratic Party (PDP) na kasa.
Channels TV ta rahoto cewa kwamitin gudanarwa na jam'iyyar PDP a gudunmar Igyorov na karamar hukumar Gboko ta jihar Benue ce ta dakatar da Ayu.
An rahoto cewa an dakatar da Ayu ne saboda zargin cin dunduniyar jam'iyyar bayan shugabannin sun kada kuri'ar rashin karfin gwiwa a kansa.
Dalilin da yasa PDP ta dakatar da shugabanta na kasa, Iyorchia Ayu
Banger Dooyum, sakataren PDP a gudunmar Igyorov da ke karamar hukumar Gboko ya ce zagon kasar da Ayu ya yi wa jam'iyyar shine babban dalilin da yasa PDP ta rasa gudunmar shugaban jam'iyyar na kasa da karamar hukumar yayin zaben da ya gabata.
Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!
Yayin da yake karanto shawarar da shugabannin gudunmar suka yanke, Dooyum ya bayyana cewa Ayu da makusantarsa basu yi zabe ba a yayin zaben gwamnan jihar na ranar 18 ga watan Mayu.
PDP ta kuma zargi Ayu da kin biyan hakokin da ya rataya a wuyansa na shekara kamar yadda yake a kundin tsarin mulkin jam'iyyar.
Takardar da ta tabbatar da dakatarwar da aka yi wa Ayu yana dauke da sa hannun shugabanni 12 cikin 17 na jam'iyyar a gudunmar Ayu, rahoton Vanguard.
Ba wai gudunmar Ayu da karamar hukumar kadai PDP ta rasa ba, jam'iyyar mai mulki a jihar ta kuma fadi a zaben gwamnan jihar inda jam'iyyar All Progressives Congress (APC) da dan takararta Father Hyacinth Alia suka yi nasara.
Zaben 2023: "Abin Da Yan Adawa Suka Shirya Yi Yayin Rantsar Da Ni", Tinubu Ya Yi Fallasa, Ya Ambaci Sunaye
Ayu da gwamnan jihar Benue, Samuel Ortom basa ga maciji tun bayan da jam'iyyar ta gudanar da zaben fidda dan takararta na shugaban kasa wanda Atiku Abubakar ya zama dan takararta a zaben wanda PDP ta sha kaye.
A wani labari na daban, tsohon gwamnan jihar Ekiti, Ayodele Fayose ya daura alhakin kalubalen da kasar ke fuskanta a kan shugabanni da yan siyasar kasar.
Asali: Legit.ng