Ku Tallafawa Mahaifina, Ba Zai Iya Shi Kadai Ba, Yar Tinubu Ta Roki Yan Najeriya

Ku Tallafawa Mahaifina, Ba Zai Iya Shi Kadai Ba, Yar Tinubu Ta Roki Yan Najeriya

  • Daya daga cikin yayan zababben shugaban kasa, Bola Tinubu ta roki yan Najeriya da su cigaba da goyawa mahaifinta baya don samun nasarar mulkinsa
  • Yar zababben shugaban kasar ta yi kiran ne yayin taron bitar Ansar-ud-Deen karo na 28 da kuma yiwa kasa addu'a ta musamman a Abuja
  • Malamai a wajen taron sun roki al'umma da su dinga taimakawa marasa karfi ko da bayan ficewar watan Ramadan don taimakawa cigaban al'umma da kasa gaba daya

FCT, Abuja - Cif Mujidat Folashe Tinubu Ojo, yar zababben shugaban kasa, Asiwaju Bola Tinubu, ta bukaci yan Najeriya da su dafawa mahaifinta ya yi nasara a shugabancin kasar zuwa matakin da kowa zai amfana, rahoton Daily Trust.

Ta yi rokon ne a ranar Lahadi a Abuja, a taron bitar azumi an kungiyar musulmi ta Ansar-ud-Deen (ADSN) karo na 28 da kuma addu'a ta musamman ga kasa, mai taken: 'Ramadan: musulunci da kyakkyawan shugabanci: hakkin musulmi da ta gudana a babban masallacin ADSN, da ke Maitama, Abuja.

Kara karanta wannan

Abin Da Ya Zama Dole Tinubu Ya Fara Yi Da Zarar An Rantsar Da Shi, Festus Keyamo Ya Bayyana

Tinubu
Ku Tallafawa Mahaifina, Ba Zai Iya Shi Kadai Ba, Yar Tinubu Ta Roki Yan Najeriya
Asali: Facebook

DUBA: Shigo shafin Legit.ng na manhajar Legit.ng na Telegram! Kada ka bari komai ya wuce ka

A cewarta, duk da an yi zabe kuma mahaifinta ya yi masa, ba hakan na nufin shikenan ba saboda yanzu ne aikin Tinubu da sauran yan Najeriya zai fara.

''Ina kira ga yan Najeriya da su yi addu'a su kuma tallafawa zababben shugaban kasa da ya gudanar da mulkinsa cikin nasara don mayar da Najeriya abar alfahira ga kowa. Ba zai iya shi kadai ba kuma dole yan Najeriya su goya ma sa baya, duk da an gama zabe,'' a cewarta.

Da ya ke magana akan taken bitar, shugaban kungiyar ASDN, shugaban majalisar malaman Arewa, Sheik Muhydeen Ajani Bello, ya yi gargadi kan almubazaranci tare da nemawa marasa galihu taimako don samun cigaban kasa da zaman lafiya.

''Ma su rike da madafun iko wajibi akansu dole ne su taimakawa marasa karfi, haka su ma wanda ba ma su mulki ba dole sai sun taimaka don taimakawa cigaban al'umma da kasa," in ji Bello.

Kara karanta wannan

A shirye nake: Zababben gwamnan Katsina ya fadi abin da zai a ranar da ya karbi mulki

Babban malamin musuluncin ya ce Annabi Muhammad ya ce

''Mu taimakawa mubukaci ko da kuwa shi ya na kan doki kai kuma kana tafe a kafa.''

Da ya ke jawabi tun da farko, Limamin kungiyar shiyyar Abuja, Alhaji Mohammed Kabir Olayiwola, ya ce ba sai iya watan azumin Ramadan za a taimakawa mubukata ba.

Keyamo Ya Fada Tinubu Abin Da Ya Kamata Ya Fara Yi Da Zarar An Rantsar Da Shi

Festus Keyamo, karamin ministan kwadago da samar da ayyuka kuma mai magana da yawun kwamitin kamfen din dan takarar shugaban kasa na APC, ya bayyana abin da mai gidansa, zababben shugaban kasa Bola Tinubu zai fara yi da zarar an rantsar da shi a watan Mayu.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aminu Ibrahim avatar

Aminu Ibrahim (Hausa HOD) Aminu Ibrahim leads the Hausa Desk at Legit.ng. He holds a Bachelor's degree in Microbiology from Ahmadu Bello University, Zaria, and pursued further with a Master's degree in Environmental Microbiology from Federal University Dutse, Jigawa. With over seven years of experience, Aminu has honed his craft in news reporting and content editing, weaving narratives that captivate and inspire audiences: aminu.ibrahim@corp.legit.ng or +2348030996164