Manyan Dalilai 2 Da Suka Saka Kotun Daukaka Kara Ta Tabbatar Da Adeleke A Matsayin Gwamnan Osun

Manyan Dalilai 2 Da Suka Saka Kotun Daukaka Kara Ta Tabbatar Da Adeleke A Matsayin Gwamnan Osun

FCT, Abuja - Duk da dai akwai sauran rina a kaba, a iya cewa Sanata Ademola Adeleke zai samu salama bayan da kotun daukaka kara a Abuja ranar Juma'a, 24 ga watan Maris, ta tabbatar da zabensa a matsayin gwamnan Jihar Osun.

Oyetola, gwamnan da ya mika mulki na karshe a jihar, ya na kalubalantar nasarar Adeleke, da jam'iyyar PDP a zaben 16 ga watan Yuli, 2022.

Ademola Adeleke
Magoyin bayan dan takarar PDP, Ademola Adeleke, a Osogbo, Jihar Osun yana rike da fostan kamfe ranar 15 ga watan Yulin 2022. Hoto: PIUS UTOMI EKPEI/AFP
Asali: Getty Images

Oyetola ne dai ya fara yin nasara a kotun sauraron karrarakin zabe a Osogbo

DUBA: Bibiyemu a Instagram don samun labarai masu muhimmanci kai tsaye cikin manhajar

Kotun sauraron karrarakin zabe ta yanke hukunci saboda la'akari da aringizon kuri'a a wuraren da Gwamna Adeleke ya samu mafi rinjayen kuri'u ta kuma bayyana Oyetola na jam'iyyar APC a matsayin wanda ya lashe zabe bayan ta kwashe ''haramtattun kuri'u'' daga kuri'un PDP.

Kara karanta wannan

Murna Ya Barke Yayin Da Kotun Daukaka Kara Ta Yanke Hukunci Kan Shari'ar Oyetola Na APC Da Adeleke Na PDP

Rashin amincewa da hukuncin kotun sauraron karrarakin zabe, Gwamnan ya daukaka kara, ya na rokon kotun daukaka karar da ta yi watsi da wancan hukuncin ta kuma jaddada nasararsa.

Ranar Juma'a, tawagar alkalai uku na kotun daukaka karar karkashin jagorancin Mohammed Shuaibu ta amince da bukatar Adeleke.

Alkalan sun yi watsi da wannan hukuncin na kotun karrarakin zabe wanda ya kwace nasarar gwamnan Osun a kwanakin baya cikin watan Janairu.

Ta bukaci jam'iyyar APC da Oyetola da su biya tarar N500,000.

Ga manyan dalilai uku da ya janyo kotun daukaka kara ta amince da bukatar Adeleke.

Hukuncin karshe na kotun karrarakin zabe kan aringizon kuri'a ba daidai ba ne

A hukuncin kotin daukaka karar, kotun sauraron karrarakin zabe ta yi kuskuren yanke cewa an yi aringizon kuri'a lokacin zaben gwamnan.

Ta bayyana cewa hujjar da aka yi la'akari da ita wajen yadda da batun aringizon kuri'a ya jingina ne kawai ga hujjojin APC da Oyetola, kamar yadda Premium Times ta ruwaito.

Kara karanta wannan

Jerin Abubuwa 5 Da Obi Ya Bukaci Kotun Zabe Ta Yi Masa A Yayin Da Ya Ke Kallubalantar Nasarar Tinubu

Oyetola da APC sun gaza gabatar da hujjar masu rijastar zabe da BVAS don tabbatar da da'awarsu

Kotun daukaka karar ta kuma ce Oyetola da jam'iyyar APC ''ba su gabatar da shaidar ma su rijistar zabe da kuma na'urar BVAS'' wadda ta nadi bayanan wanda aka tantance don kada kuri'a a zaben gwamnan ba.

A cewar alkalan, ko da akwai aringizon kuri'a ko babu a akwatin zabe za iya samun hujja ne kadai ta hanyar bincika shaidar da ke rijistar ma su zabe da kuma na'urar BVAS.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aminu Ibrahim avatar

Aminu Ibrahim (Hausa HOD) Aminu Ibrahim leads the Hausa Desk at Legit.ng. He holds a Bachelor's degree in Microbiology from Ahmadu Bello University, Zaria, and pursued further with a Master's degree in Environmental Microbiology from Federal University Dutse, Jigawa. With over seven years of experience, Aminu has honed his craft in news reporting and content editing, weaving narratives that captivate and inspire audiences: aminu.ibrahim@corp.legit.ng or +2348030996164