Fayose Ya Yi Kakkausan Kalamai, Ya Fallasa Wadanda Suka Jefa Najeriya Cikin Matsala

Fayose Ya Yi Kakkausan Kalamai, Ya Fallasa Wadanda Suka Jefa Najeriya Cikin Matsala

  • Tsohon Jihar Ekiti, Ayodele Peter Fayose, ya koka kan halin da Najeriya da mutanenta ke ciki
  • Fayose ya ce yan siyasa da ma su ruwa da tsaki ne su ka jefa Najeriya halin da ta ke ciki yanzu
  • Ya bayyana cewa kasar a tsaye ta ke chak babu wani cigaba tun jamhuriyya ta biyu a 1978

Tsohon gwamnan Ekiti mai yawan surutu, Ayodele Fayose, ya ce yan siyasa da ma su madafun iko ya kamata a zarga kan halin rashin cigaba da Najeriya ke fama da shi a matsayin kasa.

Osokomole, kamar yadda magoya bayansa su ke kiran shi, ya bayyana haka a wata hira ranar Alhamis, 23 ga watan Maris, a gidan talabijin na Arise TV a shirin barka da safiya, The Morning Show.

Ayo Fayose
Fayose ya yi kakkausan kalamai, ya bayyana wanda ke jefa Najeriya a matsala. Hoto: Photo: @GovAyoFayose
Asali: UGC

Kara karanta wannan

Tsohon Gwamna Ya Yi Wa PDP Raddi Mai Ban Tsoro Bayan Dakatar da Shi Daga Jam’iyya

DUBA: Shigo shafin Legit.ng na manhajar Legit.ng na Telegram! Kada ka bari komai ya wuce ka

Ayodele Fayose ya ce Najeriya a tsaya ta ke tun bayan jamhuriyya ta biyu.

A cewar Fayose, ba abin da ya canja tun 1979, ya na mai cewa dole a zargi yan siyasa kan rashin cigaban da ya addabi Najeriya.

An jiyo Fayose, kamar yadda jaridar Punch ta ruwaito ya na cewa:

''Akwai abubuwan rashin daidai da ke addabar Najeriya. Tun 1979, ba abin da ya canja. Na dora mafi yawan matsalolin kan sakacin yan siyasa da ma su rike da madafun iko.
''Idan ka tambayi (Muhammadu) Buhari a 2015, idan ka fadi zabe, za ka karbi rashin nasara?' cewa ya ke 'Ni zan yi nasara'. Bai taba cewa zai karbi faduwa ba.''

Ya kuma fallasa yadda yan majalisu su ka gaza kare kasar yayin da ya bayyana siyasar kasar a matsayin ''gurbatacciya''.

Kara karanta wannan

Fayose Ya Yi Zazzafan Martani, Ya Bayyana Wadanda Ke Da Hannu a Matsalolin Najeriya

Fayode ya ce:

''Na fada mu ku sanatoci, yan majalisar wakilai za su koma zauren majalisa. Tsarin ya gurbace. Ba wanda ya ke kare shi.
''Sai dai a yi ta zargin hukumar zabe mai zaman kanta ta kasa INEC, ya kamata mu ja jan layi kamar sojoji. Babu wata matsala a zabe.''

'Zaben 2023: Ba zan taba zama dan APC ba, cewar Fayose

A wani bangaren, Ayo Fayose ya jaddada cewa baya nadamar kin komawa APC.

Fayose ya bayyana haka ne bayan goyon bayan takarar Tinubu maimakon dan takarar jam'iyyarsa ta PDP, Atiku Abubakar.

Jigon PDP ya ce shi cikakken mutum ne bayan da ya yi gwamna q jiharsa har karo biyu.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aminu Ibrahim avatar

Aminu Ibrahim (Hausa HOD) Aminu Ibrahim leads the Hausa Desk at Legit.ng. He holds a Bachelor's degree in Microbiology from Ahmadu Bello University, Zaria, and pursued further with a Master's degree in Environmental Microbiology from Federal University Dutse, Jigawa. With over seven years of experience, Aminu has honed his craft in news reporting and content editing, weaving narratives that captivate and inspire audiences: aminu.ibrahim@corp.legit.ng or +2348030996164