“Babu Abun da Ya Sauya Tun 1979”: Fayose Ya Daura Laifin Halin Da Najeriya Ke Ciki Kan Yan Siyasa
- Tsohon gwamnan jihar Ekiti, Ayodele Fayose, ya koka kan halin da Najeriya da mutanen ta ke ciki a yanzu
- Fayose ya ce yan siyasa da masu ruwa da tsaki sune suka haddasa matsalar da Najeriya ke ciki a yanzu haka
- Ya bayyana cewa Najeriya na nan a durkushe ta bangaren ci gaba tun karni na biyu a 1979
Tsohon gwamnan jihar Ekiti, Ayodele Fayose ya ce yan siyasa da masu ruwa da tsaki a harkar siyasa ya kamata a rike kan rashin ci gaba a kasar.
Fayose ya bayyana hakan ne yayin wata hira a shirin Arise TV na "The Morning Show" a ranar Alhamis, 23 ga watan Maris.
A cewar Fayose, babu abun da ya chanja tun 1979 yayin da ya bayyana cewa yan siyasa sune ke da alhaki a matsalar da ke tunkarar kasar a yanzu.
Jaridar Punch ta nakalto Fayose yana cewa:
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
"Abubuwa da yawa na damun Najeriya. Tun 1979, babu abun da ya chanja. Na daura yawancin laifi na matsalolin kan masu ruwa da tsaki da yan Najeriya.
"Idan kuka tambayi (Muhammadu) Buhari a 2015, idan ka fadi zabe, za ka yarda da shan kaye? sai ya ce 'zan ci zabe'. Bai taba yarda zai fadi ba."
Bangaren dokoki ma suna da laifi, Fayose
Ya kuma caccaki bangaren dokoki kan gazawarsu wajen kare kasar yayin da ya bayyana tsarin siyasar Najeriya a matsayin "mara lafiya".
Fayose ya ce:
"Na fada maku sanatoci, yan majalisar wakilai na komawa majalisar dokoki. Tsarin bai da lafiya. Babu wanda ke kare shi.
"Maimakon ganin laifin hukumar zabe ta kasa mai zaman kanta, akwai bukatar mu shata jan layi kamar sojoji."
Ba zan taba komawa APC ba, Inji Fayose
A wani labarin kuma, mun ji a baya cewa tsohon gwamnan jihar Ekiti, Ayodele Fayose ya nanata cewa ba zai taba sauya sheka zuwa jam'iyyar APC mai mulki ba.
Fayose wanda ya marawa zababben shugaban kasa, Bola Tinubu baya a zaben shugaban kasa na 2023 ya ce ya yi hakan ne saboda ya yarda cewa ya kamata mulki ya koma yankin kudancin kasar.
Jigon na PDP dai ya nuna adawa da dan takarar jam'iyyarsa, Atiku Abubakar a zaben inda ya marawa dan APC baya.
Asali: Legit.ng