“Allah Na Tare Da Ni”: Gwamna Fintiri Ya Yi Martani Cike Da Karfin Gwiwa Kan Zaben Adamawa

“Allah Na Tare Da Ni”: Gwamna Fintiri Ya Yi Martani Cike Da Karfin Gwiwa Kan Zaben Adamawa

  • Gwamna Umaru Fintiri ya nuna karfin gwiwar cewa za a ayyana shi a matsayin wanda ya lashe zaben gwamnan jihar Adamawa
  • Fintiri wanda ke neman zarcewa a kan kujerarsa ya ce bai damu da halin da ake ciki ba a yanzu
  • Ya bayyana cewa yana da yakinin cewa Allah zai sa nasara ya zo wajensa kuma mutanen Adamawa za su sake zabensa

Dan takarar jam'iyyar Peoples Democratic Party (PDP) kuma gwamna mai ci a jihar Adamawa, Umaru Fintiri, ya ce bai damu da tsarin ayyana zaben gwamnan jihar a matsayin wanda bai kammalu ba da aka yi.

Jaridar Vanguard ta rahoto cewa Fintiri ya bayyana hakan ne a wata hira da ya yi da sashin Hausa na BBC a ranar Laraba, 22 ga watan Maris.

Gwamna Fintiri da Aisha Binani
“Allah Na Tare Da Ni”: Gwamna Fintiri Ya Yi Martani Cike Da Karfin Gwiwa Kan Zaben Adamawa Hoto: Gov Umaru Fintiri and Senator Aishatu Dahiru
Asali: Facebook

Gwamnan mai ci ya ce yana da yakinin cewa Allah na tare da shi kuma ya ba da tabbacin cewa mutanen jihar Adamawa za su yi zabi nagari sannan su zabi zarcewarsa.

Kara karanta wannan

Da Gaske Abba Gida-Gida Ya Ce Zai Rushe Masarautun Kano? Zababben Gwamnan Kano Ya Fadi Gaskiyar Lamari

Fintiriya ce:

DUBA: Bibiyemu a Instagram don samun labarai masu muhimmanci kai tsaye cikin manhajar

"Muna jiran lokacin da za a kammala zaben da kuma ayyana wanda ya yi nasara."

A cewersa ko kadan halin da ake ciki a yanzu bai firgita shi ba yayin da ya bayyana cewa maimaicin abun da ya faru a baya ne, kuma Allah zai sa ya yi nasara.

Ya ce:

"A wannan karon Allah zai maimaita tarihi nasara ya zo gareni. Mutanen Adamawa za su yanke hukunci sannan su yi mani ruwan kuri'u. Ina da yakinin nine zan samu mafi rinjayen kuri;u idan Allah ya yarda. Ban damu ba, na yarda da Allah madaukakin sarki wanda zai tabbatar da lokacin da ya dace da za a ayyana ni a matsayin wanda ya yi nasara."

A ranar Litinin, 20 ga watan Maris, hukumar zabe ta kasa mai zaman kanta (INEC) ta ayyana zaben gwamnan jihar Adamawa a matsayin wanda bai kammalu ba.

Kara karanta wannan

2023: Jerin Jihohin da Ba'a Kammala Zaben Gwamna Ba da Waɗanda INEC Ta Dakatar da Tattara Sakamako

Kafin INEC ta ayyana hakan, Gwamna Fintiri ya samu kuri'u 421,524, yayin da babbar abokiyar hamayyarsa, Sanata Aishatu Dahiru Binani ta jam'iyyar APC ta samu kuri'u 390,275.

A wani labarin, dan takarar jam'iyyar LP a zaben shugaban kasa na 2023 da aka yi, Peter Obi ya bukaci hukumar zabe da ta gaggauta sanar da sakamakon zaben gwamna a jihohin Abia da Enugu.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Musa avatar

Aisha Musa (Hausa writer) Aisha Musa 'yar jarida ce wacce ta kwashe shekaru biyar tana aikin gogewa a harkar yada labarai. Ta kammala karatun ta a Jami'ar Ibrahim Badamasi Babangida (IBB Lapai) a shekarar 2014 tare da digirin farko a fannin Tarihi. Aisha Editan Hausa ce wacce ke amfani da kwarewa da kwazonta don karfafawa wasu gwiwar yin aiki tukuru don cimma nasara. Ta karbi lambar yabo na gwarzuwar shekarar 2021 a bangaren Hausa na Legit. Za ku iya aika mata sakonnin imel ta adireshinta aisha.musa@corp.legit.ng