Gwamna Dapo Abiodun Ya Lashe Zaben Gwamnan Jihar Ogun a APC
- Jam'iyyar APC mai mulki ta ci gaba da jan zarenta a jihar Ogun bayan bayyana sakamakon zaben gwamna daga bakin INEC
- Hukumar zaɓe mai zaman kanta ta ƙasa (INEC) ta sanar da gwamna Dapo Abidoun a matsayin wanda ya samu nasara
- Zaben dai ya yi zafi matuka tsakanin manyan jam'iyyun siyasa biyu watau APC da PDP, kuma tazarar ba ta da yawa a tsakaninsu
Ogun - Hukumar zaɓe mai zaman kanta ta ƙasa (INEC) ta ayyana Dapo Abiodun na jam'iyyar All Progressives Congress (APC) a matsayin wanda ya lashe zaɓen gwamnan jihar Ogun.
Baturen zaɓe na jihar, Farfesa Kayode Adebowale, ya sanar da wanda ya samu nasara bayan kammala tattara sakamako daga kananan hukumomi 20 da ke faɗin jihar.
Ya ce gwamna Abiodun, wanda ya nemi ta zarce a inuwar APC, ya samu kuri'u 276,298, hakan ya ba shi nasarar lallasa babban abokin karawarsa na jam'iyyar PDP, Ladi Adebutu, wanda ya tashi da kuri'u 262,383.
Ɗan takarar gwamna a inuwar jam'iyyar African Democratic Congress (ADC), Biyi Otegbeye, ne ya zo na uku da tazara mai nisa sosai, kamar yadda Daily Trust ta ruwaito.
DUBA: Shigo shafin Legit.ng na manhajar Legit.ng na Telegram! Kada ka bari komai ya wuce ka
Gwamna Abidoun na cikin jerin gwamnonin APC da suka nemi ta zarce kato na biyu kan madafun iko kuma Allah ya ba su nasara a zaɓen da aka kammala ranar Asabar.
A ranar 18 ga watan Maris, 2023 aka gudanar da zaben gwamna da 'yan majalisun jiha a jihat Ogun da sauran jihohin Najeriya 27, kamar yadda Punch ta ruwaito.
Zaɓen ya yi zafi a jihohi da dama kamar Kaduna, Kano, Sakkwato, Delta, Ogun da sauran wasu jihohi. INEC na ci gaba da sanar da waɗanda suka samu nasara bayan gama tattara alƙaluma.
Kauran Bauchi ya lashe zabe
A wani labarin kuma bayan kammala tattara sakamako, INEC Ta Bayyana Sakamakon Zaben Gwamnan Bauchi
Baturen zabe a jihar Bauchi da ke arewa maso gabashin Najeriya ya ayyana ɗan takarar PDP a matsayin wanda ya lashe zaben gwamna.
Gwamna Bala Muhammed na PDP wanda ke neman tazarce ya samu nasara ne bayan samun kuri'u mafi rinjaye a zaɓen ranar Asabar.
Asali: Legit.ng