Abdulrahman Abdulrazaq Ya Lashe Zaben Gwamnan Kwara, Ya Yi Nasara A Dukkan Kananan Hukumomi 16

Abdulrahman Abdulrazaq Ya Lashe Zaben Gwamnan Kwara, Ya Yi Nasara A Dukkan Kananan Hukumomi 16

Hukumar zabe mai zaman kanta INEC, a ranar Lahadi ta ayyana Gwamna Abdulrahman Abdulrazaq na Jihar Kwara na jihar a matsayin wanda ya lashe zaben gwamna na jihar ta shekarar 2023.

Gwamnan ya yi nasarar lashe zabuka a dukkan kananan hukumomi 16 na jihar kamar yadda baturen zabe na jihar, Farfesa Isaac Itodo, shugaban jami'ar Makurdi, jihar Benue ya sanar.

Abdulrazaq wanda ya yi takara a karkashin jam’iyyar APC, ya lashe zaben gwamnan jihar da aka gudanar a ranar Asabar da ta gabata inda ya samu kuri’u 273,424 inda ya doke abokin karawarsa Yaman Abdullahi na jam’iyyar PDP wanda ya samu kuri’u 155,490 a zaben.

INEC, a daren ranar Asabar ta fara sanar da sakamakon zabukan inda ta sanar da na kananan hukumomi uku na Ekiti, Isin da Offa.

A lokacin da aka cigaba da sanar da sakamakon zaben a safiyar ranar Lahadi, aka cigaba har zuwa yamma, kuma daga bisani aka sanar gwamnan ya lashe sauran kananan hukumomi 13.

Ga sakamakon zaben dalla-dalla a kasa:

Sakamakon zaben gwamna daga kananan hukumomin jihar Kwara

Ilorin West LGA

APC - 46,468

PDP - 32,372

Baruten LGA

APC - 28,060

PDP - 7,987

Edu LGA

APC - 22,458

PDP - 17,378

Kaiama LGA

APC - 14,431

PDP - 6,297

Asa LGA

APC - 14,946

PDP - 11,183

Ilorin South LGA

APC - 20,148

PDP - 12,096

Oyun LGA

APC - 8,991

PDP - 5,465

Oke Ero LGA

APC - 7,758

PDP - 3,768

Sakamakon zabe daga Nigerian Tribune

Sakamakon zaben gwamna daga kananan hukumomin jihar Kwara

Isin LGA

APC 5,274

PDP 3,400

Ekiti LGA

APC 6,836

PDP 4,273

Offa LGA

APC 14,696

PDP 6,705

Irepodun LGA

APC 12,860

PDP 7,614

Patigi LGA

APC 13,813

PDP 6,544

Moro LGA

APC 15,161

PDP 6,823

Ilorin East LGA

APC 23,925

LP 129

Ifelodun LGA

APC 17,599

PDP 9,085

Sakamakon zaben na zuwa ke kamar yadda gidan talabijin na Channels ya tattaro.

Authors:
Aminu Ibrahim avatar

Aminu Ibrahim (Hausa HOD) Aminu Ibrahim leads the Hausa Desk at Legit.ng. He holds a Bachelor's degree in Microbiology from Ahmadu Bello University, Zaria, and pursued further with a Master's degree in Environmental Microbiology from Federal University Dutse, Jigawa. With over seven years of experience, Aminu has honed his craft in news reporting and content editing, weaving narratives that captivate and inspire audiences: aminu.ibrahim@corp.legit.ng or +2348030996164