Dalilin da Yasa Na Kusa Kuka Lokacin da Na Zama Mataimakin Shugaban Kasa, Jonathan
- Goodluck Jonathan ya baiwa yan siyasa shawara mai kyau kuma mai jan hankali game da burikansu na shugabantar al'umma
- Tsohon shugaban kasan ya ce bai taba tunanin zama mataimaki ba lokacin da aka zabe shi abokin takarar marigayi Yar'adua
- Ya ce amma kaddara ce daga Allah, don haka ya nemi 'yan siyasa su zama masu son zaman lafiya
Bayelsa - Tsohon shugaban kasa, Goodluck Jonathan, yace bai taɓa kaunar zama mataimakin shugaban kasa ba lokacin da aka zaɓe shi abokin takarar marigayi Umaru Musa Yar'adua.
Jonathan ya ƙara da cewa ya yi kuka sakamakon haka amma dole ta sa ya ɗauki lamarin a matsayin kaddara daga Allah, kamar yadda Channels tv ta ruwaito.
Ya shawarci 'yan siyasa da su zama masu son zaman lafiya lokacin da kuma bayan babban zaben 2023.
Tsohon shugaban kasan ya faɗi haka ne yayin da ya kai ziyarar ta'aziyya ga gwamna Douye Diri na jihar Bayelsa, wanda ya rasa mahaifinsa.
DUBA: Bibiyemu a Instagram don samun labarai masu muhimmanci kai tsaye cikin manhajar
A kalamansa ya ce:
"A matsayin shugaba a ƙasar nan, wanda ya samu damar aiki a matakin jiha da ƙasa, abinda zan iya cewa kaɗai shi ne siyasa ba dole sai ka samu nasara ba. Idan Allah ya so zaka yi nasara amma idan ba lokacinka bane, ba zaka kai ba."
"Lokacin da na zama mataimakin shugaban kasa sai da na yi kuka, ban taba tunanin zan kai matsayin ba, amma Allah ya tsara kaddarata a haka shiyasa na tafi."
"Ina shawartar waɗanda ke sha'awar shiga Ofisoshin nan da magoya bayansu su kiyaye kansu, mu suke son yi wa aiki ba kansu ba. A ko da yaushe ina faɗin idan kana burin shiga majalisa, mutane suka ce basu sonka, koma ka kwanta abinka."
Jonathan ya ƙara da bayanin cewa duk wanda ke son yi wa al'umma aiki ya kamata ya zama mai hali na kwarai, bai dace ya kashe mutane kafin musu aiki ba.
"Saboda haka wajibi mutane su zama masu son zaman lafiya, Idan Allah ya kaddara zasu ci zaɓe, ba wanda ya isa ya hana, su zasu lashe zabe " inji shi
Buhari ya ƙara naɗa mutane 7
A wani labarin kuma Shugaba Muhammadu Buhari Ya Rantsar da Mutane 7 da Ya Naɗa Mukamai
Gabanin fara taron majalisar zartaswa ta tarayya (FEC), shugaban Najeriya ya baiwa wasu mutanr Bakwai rantsuwar kama aiki bayan sabunta naɗinsu a muƙamai.
Asali: Legit.ng