Jiga-Jigan APC Sun Yi Watsi Da Gbajabiamila, Sun Bukaci Tinubu Ya Zabi Faleke a Matsayin Shugaban Ma’aikata
- Wasu jiga-jigan APC sun nuna sha'awarsu na son Hon. Abiodun Faleke ya zama shugaban ma'aikata
- Faleke mai shekaru 63 ya kasance mamba mai wakiltan mazabar Ikeja a majlisar wakilai
- Koda dai ya fito daga jihar Kogi, Faleke na taka rawar gani sosai a siyasar jihar Lagas kuma ya kasance na hannun damar Tinubu
Abuja - Babbar jagora a jam'iyyar All Progressives Congress (APC) Hajiya Sa’adatu Garba Dogon Bauchi ta bukaci zababben shugaban kasa Bola Tinubu da ya nada Hon. Abiodun Faleke a matsayin shugaban ma'aikata idan aka rantsar da shi.
Dogon Bauchi, wacce ta yi rokon a cikin wata budaddiyar wasika zuwa ga Tinubu wanda jaridar Leadership ta samu, ta tunatar da zababben shugaban kasar cewa Faleke ya kasance tare da shi a shekaru 30 da ya yi yana son zama shugaban kasa.
Ta rubuta:
"Ya mai girma, mun rubuta wasikar don rokon kujerarka mai karamci cewa kada ka manta da magoya bayanka na APC wadanda suka kasance tsare da kai tsawon shekaru da yawa a wannan tafiya. Tafiyar shekaru 30 bai kasance mai sauki ba amma yanzu ya zama gaskiya.
Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!
"Ya mai girma, duk kungiyoyin goyon bayanka na siyasa a matakin kasa, masana da kwararru da wadanda aka nada a kwamitin yakin neman zaben shugaban kasa za su ji dadi idan na hannun damarka, Hon. Abiodun Faleke zai kula da ragamar ofishin shugaban ma'aikata.
"Yana da gaskiya, cancanta, lissafi, lura, jajircewa da hangen nesa kuma yana da kwarewa a siyasa da shugabanci.
"Bugu da kari, ya yi aiki ba ji ba gani tare da kwamitin yakin neman zaben shugaban kasa da kungiyoyin goyon baya da dama don tabbatar da nasara a zaben da aka kammala, wanda ya kai ka ga yin nasara; babu wanda ya san kungoyin goyon bayan sama da shi."
Ka sauya fasalin Najeriya zuwa yanki - Gani Adams ga Tinubu
A nashi bangaren, Aare Onakakanfo na kasar Yarbawa, Iba Gani Adams, ya bukaci Tinubu da ya sauya fasalin Najeriya zuwa yanki.
Daily Post ta rahoto cewa basaraken ya yi rokon ne a bikin Oodua na 2023 wanda aka yi a jihar Lagas.
Ya ce Najeriya ta sha wahala sosai, yana mai cewa sauya fasalin kasar zuwa yanki shine mafita ga kasar nan.
Zababbun sanatoci biyar na zawarcin kujerar shugaban majalisar dattawa
A wani labarin, mun ji cewa wasu daga cikin zababbun yan majalisa da suka samu damar komawa majalisar tarayya ta 10 sun fara kamun kafa a wajen takwarorinsu don zama shugaban majalisar dattawa.
Asali: Legit.ng