2023: Dan Takarar Gwamnan Oyo Na SDP Ya Janyewa Gwamna Makinde
- Jam'iyyar PDP ta samu ƙarin goyon baya daga ɗan takarar gwamna a inuwar SDP a jihar Oyo
- Mista Lana, mai neman zama gwamnan Oyo a zabe mai zuwa ya hakura da takara domin goyon bayan gwamna Makinde
- Wannan na zuwa ne kwanaki huɗu gabanin zaben gwamna wanda zai gudana ranar 18 ga watan Maris, 2023
Oyo - Ɗan takarar gwamna karkashin inuwar Social Democratic Party (SDP) a jihar Oyo, Mista Michael Lana, ya janye daga takara ana kwana huɗu gabanin zaɓe.
Jaridar The Nation ta rahoto cewa ɗan takarar gwamna yan janye ne domin ya koma bayan gwamna Seyi Makinde, na jam'iyyar PDP, wanda ke neman tazarce.
Mista Lana ya zama mutum na farko da ya ayyana goyon bayansa ga Makinde daga cikin 'yan takarar jam'iyyun adawa da ke hangen kujerar gwamnan Oyo ranar Asabar mai zuwa.
"Ba a Taba Lusarin Gwamna Irin Zulum Ba, Bai Cancanci Komawa Kan Mulki Ba", Ɗan Takarar NNPP Ya Dau Zafi
Jaridar Punch tattaro cewa wasu daga cikin shugabannin SDP, har da mambobin kwamitin zartaswa sun ayyana goyon bayan ɗan takarar gwamnan APC, Sanata Teslim Folarin, a makon da ya shige.
DUBA: Shigo shafin Legit.ng na manhajar Legit.ng na Telegram! Kada ka bari komai ya wuce ka
Da yake jawabi ga 'yan jarida a Ibadan ranar Talata, Lana ya yi zargin cewa wasu daga cikin jagorrin SDP sun sayar da ƙimarsu, sun ayyana goyon baya ga ɗan takarar jam'iyyar adawa.
Ya ce da yawansu gaban kansu suka yi, suka koma bayan wani ɗan takara ba tare da amincewar sauran masu ruwa da tsakin jam'iyyar SDP ba.
Meyasa dan takarar ya zabi goyon bayan Makinde?
Mista Lana ya ce bayan dogon nazari da zaman neman shawari daban-daban, masu ruwa da tsakin SDP sun cimma matsayar mara wa gwamna Makinde baya.
A kalamansa ya ce:
"Gwamna Makinde na neman agaji daga duk wani mai kishi a ciki da wajen jihar Oyo domin haɓaka jihar zuwa inda take mafarkin zuwa, kuma mun yarda zamu taimaka masa ya samu nasara."
"Sakamakon haka, mun cimma matsayar sanar da dumbin magoya bayan mu su fito kwansu da kwarkwata su zabi mai girma gwamna Seyi Makinde na PDP ranar Asabar 18 ga watan Maris."
A wani labarin kuma Sakataren PDP Na Jihar Ondo Ya Yi Murabus, Jam'iyyar Ta Yi Martani Mai Zafi
Jam'iyyar PDP ta shiga matsala mai girma sakamakon yawan murabus da sauya sheka daga cikinta a yan kwanakin nan a jihar Ondo.
Da yake tsokaci kan ci gaban, mai magana da yawun jam'iyyar na jihar ya ce ko kaɗan PDP ba ta girgiza ba kuma tana da labarin abinda ke wakana.
Asali: Legit.ng