Buhari Bai Taɓuka Komai Ba, Bai San Makamar Aiki Ba, Sanata Rufa'i Hanga
- Shugaba Muhammadu Buhari bai tabuka komai ba kuma bai san makamashin aiki ba kwata-kwata a cewar Sanata Rufai Hanga
- Hanga ya ce bayan kammala wa'adinsa, Shugaba Buhari zai koma gida a Daura ya rika barci hankali kwance domin bai ma san abin da ke faruwa a kasa ba
- Tsohon shugaban na CPC ya ce ba a taba 'lalataccen' shugaban kasa irin Buhari ba duk da cewa shi ya na yi wa kansa kirari cewa ya fi dukkan sauran shugabannin Najeriya
Sanata Rufa'i Hanga, shugaban tsohuwar jam'iyyar CPC na farko, kuma zababben sanata na mazabar Kano Central a karkashin jam'iyyar New Nigeria Peoples Party, NNPP, ya ce Shugaba Muhammadu Buhari ya gaza.
Yayin wata hira da aka yi da shi a shirin Daily Politics da Legit.ng Hausa ta yi ido hudu da bidiyon, Hanga ya ce idan Buhari ya kammala mulki zai koma Daura ya yi kwanciyarsa lafiya kalau domin bai san abin da ke faruwa ba.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Buhari ya gaza, ba a taba shugaban kasa mara sanin makamashin aiki kamansa ba, Rufai Hanga
Da ya ke amsa tambaya kan abin da ya ke ganin Buhari zai koma da shi Daura bayan wa'adinsa ya cika, shin zai yi barci hankali kwance, Hanya ya ce:
"Eh, tabbas zai yi barcinsa lafiya saboda bai san abin da ke faruwa ba. Bai san makamashin aiki ba, bai san makamashin aiki ba kuma gaskiya ne.
"Idan mutum zai gaza irin yadda ya yi, ya mayar da kasar inda ta ke a yanzu amma ya cigaba da bugun kirji yana cewa shine shugaba mafi kwazo da aka taba yi a tarihin Najeriya. Abin da ya ke cewa kenan."
A yayin da ya ke kwatanta Shugaba Buhari da sauran shugabannin Najeriya, Sanata Hanga ya ce Buhari bai tabuka komai ba kuma ya gaza.
Daga Karshe, Shugaba Buhari Ya Yi Magana Kan Amfani da Tsoffin Kudi N500 da N1000 Bayan Umarnin Kotu
Kalamansa:
"Ba abin da ya tabuka, ya gaza baki daya."
A baya-bayan nan ne kotun koli ta tabbatar da Rufai Hanga a matsayin zababben dan sanata na Kano Central karkashin jam'iyyar NNPP.
Kotun ta kuma cire tsohon gwamnan Kano, Malam Ibrahim Shekarau a matsayin dan takarar sanatan NNPP a zaben ranar 25 ga watan Fabrairu.
Asali: Legit.ng