Gwamnan CBN Ya Musanta Rahoton Cewa Yan Kulla Wa Tinubu Makarkashiya
- Gwamnan babban banki CBN ya karyata labarin da ke nuna ya shiryawa Tinubu sabon tuggu gabanin zaben gwamna
- A wata sabuwar sanarwa da kakakin CBN ya fitar, ya ce gwamna Emefiele ba ɗan siyasa ne bane kuma bai da alaƙa da ita
- Kafin wannan karin haske, an wallafa labarin cewa Emefiele ya sake shirya yi wa zababben shugaban ƙasa zagon ƙasa
Abuja - Gwamnan babban bankin Najeriya (CBN), Godwin Emefiele, ya musanta labarin da ke nuna cewa ya fara kulla wa shugaban ƙasa mai jiran gado, Bola Tinubu, sabuwar makarkashiya.
Mista Emefiele, ya kira labarin wanda jaridar The Nation ta wallafa ranar Litimin 13 ga watan Maris, 2023, da ƙarya mara tushe balle makama.
Gwamnan ya yi wannan jawabi ne a cikin wata sanarwa mai ɗauke da sa hannun Daraktan sashin sadarwa na CBN, Isa Abdulmumin, kamar yadda Vanguard ta rahoto.
Sanarwan ta ce:
DUBA: Shigo shafin Legit.ng na manhajar Legit.ng na Telegram! Kada ka bari komai ya wuce ka
"An ja hankalin CBN game da wani labari da jaridar The Nation ta buga ranar Litinin 13 ga watan Maris, 2023, wanda ya yi zargin Mista Emefiele ya ɓullo da sabon shirin yaƙar zababben shugaban kasa."
"Labarin ya yi ikirarin cewa gwamnan CBN ya tura wa wani ɗan takara makudan kudaɗe domin tunkarar babban zaben gwamnoni ranar 18 ga watan Maris, 2023."
"Muna sanar da ɗaukacin 'yan Najeriya cewa labarin ƙarya ce kuma fasadi ne domin gwamnan CBN bai da masaniya kuma bai gana ko ya zanta da Gbadebo Rhodes-Vivour, ba."
Emefiele ba ɗan siyasa bane - CBN
Bugu da ƙari, Sanarwan ta bayyana cewa gwamnan babban banki ba ɗan siyasa ben kuma ba shi da alaƙa da siyasa, bisa haka ta yi kira ga duk me ja da haka ya bayyana gaskiya.
"Don haka, ya kamata a kyale gwamna da sauran 'yan tawagarsa su maida hankali kan aikinsu domin sauke nauyin da ke kan CBN."
A wani labarin kuma Jam'iyyar APC Ta Kori Tsohon Kwamishina Bayan Gano Yana Mata Zagon Kasa
APC mai mulki ta aike da wasiƙar kora daga inuwar jam'iyyar ga tsohon kwamishinan tarayya a jihar Imo.
Lamarin dai ya haddasa ruɗani da mamaki a tsakanin magoya baya amma jam'iyyar ta fito ta kare kanta.
Asali: Legit.ng