An Nemi Shugaban APC Na Ƙasa Yayi Murabus Daga Muƙamin Sa
- Shugaban jam'iyyar All Progressives Congress (APC) na ƙasa, Abdullahi Adamu, na shan matsin lamba kan yayi murabus daga muƙamin sa
- Wata ƙungiya ta bi sahun mutanen dake kiran Abdullahi Adamu yayi murabus daga muƙamin sa na shugaban APC
- Ƙungiyar tayi ƙarin haske kan dalilan da take ganin sun isa su sanya Adamu yayi bankwana da muƙamin sa
Abuja- Wata ƙingiya mai suna Conference of Nigeria Civil Rights Activists (CNCRA), tayi kira ga shugaban jam'iyyar APC na ƙasa, Sanata Abdullahi Adamu, da yayi biyayya da kiran da akayi masa na yayi murabus daga muƙamin sa.
A cewar ƙungiyar saukar sa daga muƙamin sa zai tabbatar da daidaito, adalci da kuma gaskiya. Rahoton Tribune
Ƙungiyar CNCRA tace saukar Adamu daga muƙamin sa na shugaban jam'iyyar APC na ƙasa, zai tabbatar da samar da gwamnati wacce ta tafi da kowane ɓangare a mulkin gwamnatin Tinubu.
Ƙungiyar ta bayar da wannan shawarar ne a wata sanarwa da shugaban ta, Pastor Ifeanyi Odili, da sakataren ra Engr. Sina Akadiri, suka fitar a ranar Lahadi a birnin tarayya Abuja. Rahoton New Telegraph
DUBA: Bibiyemu a Instagram don samun labarai masu muhimmanci kai tsaye cikin manhajar
Ƙungiyar tace murabus ɗin Adamu zai ba jam'iyyar APC damar rage raɗaɗin da Kiristoci ke ji kan tikitin Muslim/Muslim na jam'iyyar a zaɓen shugaban ƙasa.
CNCRA ta yabawa mataimakin shugaban jam'iyyar APC na ƙasa na yankin Arewa maso Gabas, Mallam Salihu Lukman, kan kiran da yayi na Adamu yayi murabus daga muƙamin sa.
Wani ɓangare na sanarwar na cewa:
“Yakamata Adamu ya bi hanyar dattako da mutuntaka ta hanyar yin murabus bayan zaɓen gwamnoni da na ƴan majalisun dokokin jihohi."
“Kiristoci za su yi farin ciki da jindaɗin hakan sannan kuma hakan zai sanya yankin Arewa ta tsakiya ya samu shugaba ko mataimakin shugaban majalisar dattawa a majalisar dattawa ta 10."
Ƙungiyar CNCRA tace ta yaba da gagarumar gudunmawar da Adamu da yankin Arewa ta tsakiya ya bayar a zaɓen shugaban ƙasa da na ƴan majalisun tarayya da aka kammala kwanan nan.
Tayi nuni da cewa jam'iyyar APC mai mulki yakamata ta sakawa yankin ta hanyar tabbatar da cewa wani babban sanatan yankin ya zama shugaba ko mataimakin shugaban sabuwar majalisar dattawa ta 10.
Jam'iyyar APC Zata Sanya Labule Da Zababbun Ƴan Majalisun Ta
A wani labarin na daban kuma, jam'iyyar APC ta fara shirin zaɓar shugabannin sabuwar majalisar da za a kafa.
Jam'iyyar ta kira taro da zaɓaɓɓun ƴan majalisar tarayyar ta domin cimma wannan ƙudiri.
Asali: Legit.ng