Jam'iyyar ADP Ta Fusata, Ta Dakatar da Shugaban Jam'iyya Na Kaduna
- Jam'iyyar ADP ba ta nuna rashin jin daɗinta bisa korafe-korafen data karba daga jiga-jigai a jihar Kaduna kan shugaban jam'iyya
- Sakamakon haka, kwamitin gudanarwa na ADP ta ƙasa ya rubuta masa wakiƙar dakatarwa har sai baba ta gani
- Ta ce harkokin da shugaban ADP na Kaduna ke yi sun nuna ƙarara cewa yana cin amana da zagon ƙasa
Kaduna - Action Democratic Party (ADP) ta dakatar da muƙaddashin shugaban jam'iyyar na jihar Kaduna, Umar Isa, bisa zargin cin amana da zagon ƙasa.
Wannan matakin na kunshe a wata wasika da ta samu sa hannun shugaban ADP na ƙasa, Yabaji Sani, da kuma Sakataren jam'iyya na ƙasa, Victor Fingesi.
Channels tv ta tattaro cewa wasiƙar mai ɗauke da kwanan watan 8 ga watan Maris, 2023, ta ce matakin dakatarwan zai fara aiki nan take.
Wani sashin sakon wasikar ya ce:
Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!
"Kwamitin gudanarwa na kasa ya karbi korafe-korafe daga jagorori da mambobin jam'iyyar mu na Kaduna cewa ka tsoma hannu kan wasu harkoki da suka dusashe martabar ADP."
"A daidai wannan lokaci na kakar zaɓe, wanda jam'iyyun siyasa suka maida hankali wajen tattara goyon bayan jama'a da fafutukar lashe kujeru a babban zaɓe, muna ganin abinda ka aikata cin amana ne."
"Kuma hakan ya saɓa wa tanade-tanaden kundin tsarin da aka kafa jam'iyyar mu a kai. Daga zaran wannan wasika ta riske ka, mun dakatar da kai daga matsayin shugaban riko har sai baba ta gani."
Bugu da ƙari, jam'iyyar ta bukaci dakataccen shugaban ADP ya miƙa duk wasu kayayyakin jam'iyya hannun mataimakinsa, kamar yadda Punch ta rahoto.
"Haka nan muna umartarka da cewa, ba tare da gazawa ba ka gaggauta miƙa duk wasu kayan jam'iyyar ADP da su ke wurinka hannun mataimakinka."
NNPP Ta Kori Dan Takarar Mataimakin Gwamna
A wani labarin kuma Ta Fara Karewa Kwankwaso, NNPP Ta Kori Dan Takara da Shugaban Jam'iyya a Jihar Katsina
Biyo bayan abinda ya faru ranar Alhamis, jam'iyya mai kayan marmari ta fatattaki ɗan takarar mataimakin gwanna da wasu shugabanninta a jihar Katsina.
A wata sanarwa da kakakin NNPP na jihar, Usman Kankiya, ya fitar ya lissafo manyan jiga-jigan da matakin ya shafa.
Asali: Legit.ng