Ana Saura Kasa Da Kwana 3 Zabe, Shugabar Matan PDP a Sokoto Ta Koma APC
- Siyasar Najeriya mai abin ban mamaki, mata sun fara janyo hankali kan muhimmansu a siyasar
- Hukumar INEC na cigaba da daura damarar fara raba kayayyakin aikin zabe ga kananan hukumomi
- Manyan yan takarar da zasu fafata a zaben gwamnan Sokoto sun hada da tsohon mataimakin Tambuwal da kuma sabon abokinsa
Sokoto - Ana sauran kwanaki kasa da uku zaben gwamnoni, jagorar matan jam'iyyar People’s Democratic Party (PDP) a jihar Sokoto, Hajiya Kulu Rabah, ta koma jam'iyyar All Progressives Congress (APC).
Jagorar matan ta samu kyakkaywan tarba daga wajen jagoran jam'iyyar APC a jihar Sokoto, Sanata Aliyu Magatakarda Wamakko da kuma dan takaran gwamnan jam'iyyar, Ahmed Aliyu Sokoto, rahoton DailyTrust.
Jihar Sokoto na cikin jihohin da ake sa ido game da yadda za a kaya a zaben gwamnan jihar.
Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!
Jihar Sokoto Za ta Dau Zafi
Dubi ga yadda aka fafata tsakanin jam'iyyar PDP da APC a zaben shugaban kasa a Sokoto, ana ganin zaben ranar Asabar zai yi dumi.
Jam'iyyar PDP ce tayi nasara amma da kuri'u kasa da 5000 ta zarcewa APC.
Bugu da kari, ana zargin kwamishanan INEC na tafka ya bada gudunmuwa wajen tafka magudi ranar zaben shugaban kasa 25 ga Febrairu.
Dalilin haka hukumar INEC ta dakatar da shi daga jagorantar zaben gwamna mai zuwa.
Zaku tuna cewa gwamnan jihar, Aminu Waziri Tambuwal, ya ha mulki karkashin APC amma daga bisani ya koma PDP.
A 2019 da aka zo zaben gwamna, da kyar ya sha inda yayi nasara a kuri'u bayan zagayen zabe na biyu kui'u kasa da 350.
INEC Ta Dakatar da Shugabanta Na Jihar Sakkwato Nan Take, Ta Maye Gurbinsa
A ranar Talata, labari ya yadu cewa hukumar INEC ta dakatar da kwamishananta na jihar Sakkwato, Nura Ali, wajen musharaka a zaben gwamnan jihar.
Tuni hukumar ta maye gurbinsa da sakatare da Rose Orlaran-Anthony.
Hukumar ta umurni Dakta Nura Ali ya tattara inasa-inasa ya bar ofishin hukumar har sai lokacin da aka nemesa.
Wani babban jami'in INEC ya ce Nura Ali yana mulkin kama-karya a ofishin hukumar dake jihar kuma ba za'a lamunci haka ba.
Asali: Legit.ng