Labour Party Ta Rushe Shugabanninta a Ribas Saboda Rashawa Da Din Amanar Jam’iyya
- Gagarumin rikici ya dabaibaye jam'iyyar Labour Party reshen jihar Ribas, kasa da kwanaki biyar kafin zaben gwamna
- Shugabancin LP na kasa ya yi kira ga gaggauta sallamar shugabannin jam'iyyar a Ribas
- An bukaci shugabannin jam'iyyar su sauka saboda cin dunduniyar jam'iyyar da rashawar kudi
Saboda cin amanar jam'iyya da hamdame kudaden jam'iyya, kwamitin aiki na jam'iyyar Labour Party (LP) na kasa ya rushe shugabannin jam'iyyar na jihar Ribas nan take.
Jaridar Vanguard ta rahoto cewa an yanke wannan hukunci ne a wani taron gaggawa da aka gudanar a sakatariyar jam'iyyar na kasa da ke Abuja, a ranar Talata, 7 ga watan Maris.
Dalilin sallamar shugabannin jam'iyyar
Shugaban LP na kasa, Julius Abure wanda ya sanya hannu a jawabin da ke sanar da hukuncin da suka yanke ya ce:
DUBA: Shigo shafin Legit.ng na manhajar Legit.ng na Telegram! Kada ka bari komai ya wuce ka
"Wadanda ke kan harkoki a jihar lokacin da aka sace hakkin shugabanta a fili su sauka har sai an kammala cikakken bincike kan abun da ya faru a wannan rana."
Abure ya bukaci magoya bayan Obi da su yi watsi da duk kalamai da ayyukan Pepple yana mai cewa Beatrice Itubo ce yar takarar gwamnan LP a zaben gwamna na ranar Asabar a jihar.
Ya yi gargadin cewa Labour Party bata yi maja da kowace jam'iyyar siyasa a jihar ba, rahoton Daily Post.
Jam'iyyar Labour Party ta marawa dan takarar PDP baya a zaben gwamna
Mun ji cewa jam'iyyar Labour Party (LP) da kungiyar goyon bayan Peter Obi wato Obidient Movement a Ribas sun ayyana goyon bayansu ga Sim Fubara, dan takarar jam'iyyar Peoples Democratic Party (PDP) a zaben gwamnan jihar na ranar 11 ga watan Maris.
Dienye Pepple, shugaban jam'iyyar Labour Party a jihar ya bayyana cewa sun yanke shawarar ne don adalci da daidaito a jihar.
Sauran magoya bayan Labour Party da suka bi sahun Pepple wajen marawa Fubara baya a Port Harcourt, jihar Ribas sun yi bayanin cewa yankin kudu maso gabashin jihar, inda Fubara ya fito basu taba samar da gwamna a jihar ba.
INEC ta ba zababbun sanatoci takardar shaidar cin zabe
A wani labari na daban, hukumar zabe ta kasa mai zaman kanta ta ba zababbun sanatoci takardar shaidar cin zabe a zaben da aka yi a ranar Asabar, 25 ga watan Fabrairu.
Hukumar INEC ta gabatarwa sanatocin satifiket din nasu a wani biki da aka gudanar a zauren taro na kasa da kasa da ke Abuja.
Asali: Legit.ng