"Karya Ne Ban Koma PDP Ba, Ina Nan a APC" – Inji Ministar Buhari
- Karamar ministan ma'adinai da karafa, Gbemi Saraki, ta ce rahotannin cewa ta bar APC zuwa PDP kanzon kurege ne
- Saraki ta ce har yanzu ita yar APC ce, cewa ta yi aiki wajen ganin nasarar Tinubu a jihar Kwara yayin zaben shugaban kasa na 2023
- Ministar ta kuma karyata batun hadewa da Yahman Abdullahi, dan takarar gwamna na jam'iyyar PDP a jihar Kwara
Gbemi Saraki, karamar ministar ma'adinai da karafa ta karyata batun komawarta jam'iyyar Peoples Democratic Party (PDP) gabannin zaben gwamna da na yan majalisar dokokin jiha na ranar 11 ga watan Maris.
Ministar a cikin wata sanarwa daga hadiminta, Moses Bello, ta kuma karyata batun marawa dan takarar gwamna na jam'iyyar PDP a Kwara, Yahman Abdullahi baya, rahoton Vanguard.
Gbemi Saraki ta yi aiki don nasarar Tinubu - Inji hadiminta
Bello ya kara da cewar ministar ta yi aiki ba ji ba gani don tabbatar da ganin cewa dan takarar shugaban kasa na jam'iyyar All Progressives Congress (APC), Asiwaju Bola Ahmed Tinubu, ya lashe zaben shugaban kasar na 2023 da aka kammala a jihar Kwara.
Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!
Ya bayyana cewa hakan ya kasance ne duk da dan sabani kan ayyukan gwamnatin APC a jihar game da gadon da marigayi Oloye Sola Saraki ya bari.
A cewar Bello, Saraki ta bayyana cewa har gobe ita yar APC ce a jihar Kwara da kasar, tana mai cewa bata da niyan barin jam'iyya mai nasara, rahoton Premium Times.
An nakalto Saraki na cewa:
"Idan akwai wani abu, toh ina ma aiki ne don tabbatar da nasarar gwamnatin Asiwaju/Shettima mai zuwa a ranar 29 ga watan Mayu."
Bello ya bayyana rahoton cewa Saraki ta sauya sheka a matsayin labaran karya kamar yadda ya jaddada cewa uwar dakinsa na nan a matsayin jigon APC.
Ya kara da cewar:
"Saraki mai wayar da kan jama'a ce daga matakin kasa kuma ta yi alkawarin ci gaba da biyayya ga gwamnatin shugaban kasa Buhari da gwamnatin Tinubu da Sanata Kashim Shettima mai zuwa."
Labour Party ta rushe shugabanninta a jihar Ribas
A wani labari na daban, mun ji cewa jam'iyyar Labour Party ta rushe shugabancinta a jihar Ribas yan kwanaki kafin zaben gwamna na ranar 11 ga watan Maris.
Asali: Legit.ng