Kwamishina Ya Yi Murabus Daga Mukaminsa Kwana 10 Gabanin Zaben Gwamnoni

Kwamishina Ya Yi Murabus Daga Mukaminsa Kwana 10 Gabanin Zaben Gwamnoni

  • Kwamishinan kimiyya da fasaha na jihar Gombe ya sauka daga kujerarsa saura kwanaki kasa da 10 zaben gwamnoni
  • Mista Andirya, ya ce ya dauki matakin yin murabus ne saboda an naɗa shi kwamishina ne a takarda kawai
  • Gwamna Muhammad Inuwa Yahaya na cikin gwamnonin APC da ke neman tazarce a kan kujerarsa

Gombe - Ƙasa da kwana 10 gabanin zaben gwamnoni a Najeriya, kwamishinan kimiyya da fasaha na jihar Gombe, Mista Abishai M. Andirya, ya yi murabus daga kujerarsa.

Mista Andirya, shi ne ya bayyana haka ranar Laraba 1 ga watan Maris a Ofishinsa yayin da yake zantawa da manema labarai, kamar yadda jaridar Daily Trust ta ruwaito.

Muhammad Inuwa Yahaya.
Gwamna Muhammad Inuwa Yahaya na jihar Gombe Hoto: Inuwa Yahaya
Asali: UGC

Ya ce ya yanke shawarin murabus daga matsayin mamba a majalisar zartaswan jihar, "Saboda ina matsayin kwamishina ne a takarda kaɗai."

Kara karanta wannan

"Shi Ne Daidai" Gwamna Masari Ya Yi Magana Mai Jan Hankali Bayan Tinubu Ya Ci Zaɓe

A cewarsa, gwamna ya kange kansa ba ta yadda zaka iya ganawa da shi, kuma wata uku kenan amma sau ɗaya suka haɗu da gwamna.

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Ya ce:

"Ina cikin jam'iyyar APC tun shekarar 2015 kuma bayan mun samu nasara a 2019, gwamna ya yi alƙawarin zamu yi aiki tare don taimakawa al'umma."
"Amma ba'a naɗa ni kwamishina ba sai a watan Oktoban da ya gabata lokacin garambawul a majalisar. Tun wannan lokaci na gaza taimakom mutane na saboda ina matsayin a suna kawai ba abinda nake samu."
"Na yi kokarin ganin gwamna Muhammad Inuwa lokuta da dama domin na faɗa masa damuwata amma abun ya ci tura, abokan aiki mambobin majalisar zartaswa suka faɗa mun sai a wurin taro zan iya ganinsa."

A kwafin takardar murabus din kwamishinan wacce ta shiga hannun yan jarida, Mista Andirya, ya ce matakin da ya ɗauka zai fara aiki ne daga ranar 20 ga watan Fabrairu.

Kara karanta wannan

Na Hannun Dama Ya Ba Tinubu Shawara Ya Jawo Kwankwaso da Peter Obi a Gwamnati

"Na miƙa takardan murabus ɗina makon da ya gabata, saboda haka ina godiya ga gwamna da ya bani damar yi wa jihata aiki a matsayin kwamishina tun daga ranar 1 ga watan Nuwamba."

Yan sanda sun kara kama ɗan majalisa

A wani labarin kuma Yan Sanda Sun Cafke Zababben ɗan Majalisar Tarayya Na NNPP a jihar Kano

Awanni bayan gurfanar da Ado Doguwa, jami'in hulda da jama'a na rundunar yan sandan Kano ya tabbatar da cewa suna tsare da Sani Madakin Gini.

Madakin Gini na ɗaya ɗa cikin yan takarar da suka lashe zaben mamba a majalisar tarayya karkashin inuwar NNPP a Kano.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262