Zaben 2023: Yan Sanda Sun Cafke Ɗan Majalisar Tarayya Na NNPP a Kano

Zaben 2023: Yan Sanda Sun Cafke Ɗan Majalisar Tarayya Na NNPP a Kano

  • Jami'an yan sanda sun damƙe zababben ɗan majalisar tarayya mai wakiltar Dala a jihar Kano, Sani Madakin Gini
  • Jami'in hulda da jama'a na rundunar yan sandan Kano ya ce yanzu haka yana tsare ana bincikensa kan zargin mallakar bindiga
  • A ɗazu Kotu ta umarci a tsare Ado Doguwa a gidan gyaran hali bayan bude shari'a a kansa

Kano - Rundunar yan sanda ta kama zababben ɗan majalisar tarayya mai wakiltar Dala, Sani Madakin Gini, bisa zargin mallakar bindiga ba kan ƙa'ida ba.

Channels tv ta tattaro cewa Jami'in hulɗa da jama'a na rundunar yan sandan Kano, Abdullahi Haruna Kiyawa, ne ya tabbatar da haka, ya ce a halin yanzun suna ci gaba da bincike.

Sani Madakin Gini.
Zababben ɗan majalisar NNPP, Sani Madakin Gini Hoto: Channelstv
Asali: UGC

Idan baku manta ba yan sanda sun kama shugaban masu rinjaye na majalisar wakilan tarayya, Al-Hassan Ado Doguwa a filin jirgin Mallam Aminu Kano.

Kara karanta wannan

Karin bayani: Kotu ta tura shugaban masu rinjaye, Doguwa zuwa magarkamar Kano

Kotu ta aika Doguwa gidan gyaran hali bayan an gurfanar da shi kan tuhuma 5, kisan kai, haɗa baki a aikata mugun laifi, raunata jama'a da sauransu.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Legit.ng hausa ta fahimci cewa kama Sani Madakin Gini, wanda ya zama zaɓaɓɓem ɗan majalisar tarayya a inuwar NNPP a zaben ranar Asabar, ya ta da kura a sassan Kano.

Wasu mazauna jihar sun kaɗu da jin labarin tsare ɗan siyasan, yayin da wasu kuma suka maida martani da cewa jami'an tsaro su gudanar da bincike duk wanda aka kama a hukunta shi.

Da take tabbatar da kamen, rundunar yan sandan Kano ta bakin jami'in hulɗa da jama'a ta ce:

"Muna tabbatar da cewa Honorabul Sani Madakin Gini ya shiga hannu bisa zargin mallakar bindiga ta hanyar da ba ta dace ba. Yana tsare a hannun mu muna bincike."

Kara karanta wannan

Karin Bayani: An Gurfanar da Ado Doguwa a Gaban Kotu, Babban Abinda Ake Zarginsa Ya Fito

Kiyawa ya ƙara da cewa rundunar yan sanda ba zata yi kasa a guiwa ba a kokarinta na ganin doka ta yi aiki a kan kowa ba tare da duba matsayin mutum ba.

Daily Trust ta rahoto cewa Hotuna sun watsu a kafafen sada zumunta suna nuna ɗan siyasan kuma jigon NNPP rike da bindiga lokacin ralin karshe na Kwankwaso.

An Gurfanar da Alhassan Ado Doguwa a Gaban Kotu Kan Zargin Kisa

A wani gefen yan sanda sun gurfanar da shugaban masu rinjaye na majalisar wakilan tarayya, Al-Hassan Ado Doguwa

A ranar Talata, jami'an tsaro suka yi awon gaba da ɗan majalisar tarayyan na APC bisa zargin da haɗin bakinsa aka halaka wasu mutane uku a mazaɓarsa.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262