Datti Baba-Ahmed Ya Ce Shi Da Peter Obi Ne Suka Lashe Zaben Shugaban Kasa
- Yusuf Datti-Baba Ahmed ya magantu bayan INEC ta ayyana Bola Tinubu a matsayin zababben shugaban kasar Najeriya
- Baba-Ahmed, abokin takarar Peter Obi na Labour Party ya ce sune suka ci zaben shugaban kasa amma aka yi masu murdiya
- Dan siyasar wanda ya ce za su nemi hakkinsu a kotu, ya bukaci magoya bayansu da su sake fita a zaben gwamna da na majalisar jiha don zaben Labour Party
Dan takarar mataimakin shugaban kasa na jam'iyyar Labour Party (LP), Yusuf Datti Baba-Ahmed, ya ce shi da Peter Obi ne suka lashe zaben shugaban kasa na ranar Asabar, 25 ga watan Fabrairu.
Da yake jawabi a cikin wata sanar dauke da sa hannunsa a ranar Laraba, 1 ga watan Maris, Baba-Ahmed ya sha alwashin cewa za su kwato hakkin jam'iyyarsu, rahoton Vanguard.
Hakan na zuwa ne jim kadan bayan hukumar zabe ta kasa mai zaman kanta (INEC) ta ayyana Bola Tinubu, dan takarar shugaban kasa na jam'iyyar APC a matsayin wanda ya lashe zabe.
Ya bayyana cewa tunda har ba a tura sakamakon zabe ta na'ura ba, toh ba a yi zabe ba.
DUBA: Bibiyemu a Instagram don samun labarai masu muhimmanci kai tsaye cikin manhajar
Yayin da jam'iyyar ta yi watsi da zaben kuma magoya bayanta suka yi ikirarin cewa an yi magudi a zaben, jigon na LP ya ce ubangidansa zai yi magana a lokacin da ya dace, Channels TV ta rahoto.
Sai dai ya ba magoya bayansu cewa za su nemi doka ta yi aiki yayin da ya yi kira gare su da su kwantar da hankalinsu, yana mai cewa ba a yi zabe na gaskiya da amana ba.
Baba-Ahmed na kira ga bangaren shari'a da ta tabbatar da adalcinta idan suka isa kotu, yana mai al'ajabin ta yadda aka tattara sakamakon zaben shugaban kasa da na majalisar tarayya alhalin ba'a tura su ta na'ura ba.
Ku fita ku sake zabar Labour Party a zaben gwamna da na majalisar jiha
Ya kuma bukaci magoya bayansu da su fita su zabi jam'iyyar a zaben gwamna da na yan majalisar jiha da za a yi a ranar Asabar ta sama.
Wani bangare na jawabinsa na cewa:
"Ba tare da duba rashin karfin gwiwar da muke da shi a tsarin ba, muna rokon yan Najeriya da su fita sannan su zabi Labour Party a zaben gwamna da na yan majalisar jiha mai zuwa.
"Dokar zabe ta 2022 ta tanadi cewa za a tura sakamako ta na'ura, ba a aikata haka ba wanda ke nufin ba a yi zabe ba.
"Muna umurtan yan Najeriya da su ci gaba da sauke hakkinsu na yan kasa kamar yadda suka yi a zaben baya.
"Mun lashe zaben nan, sun ki daura sakamakon a IREV, mutanen Najeriya masu nasara ne, yan Najeriya na jiran Peter Obi da ni mu hau mulki.
"Mun lashe zaben a matsayin Labour Party, za mu kwato hakkinmu a matsayin Labour Party, za mu ceto Najeriya a matsayin Labour Party."
Obi ya kawo Legas, Delta da wasu jihohi 10 a zaben shugaban kasa
A wani labarin, Legit.ng ta kawo jerin jihohi guda 12 da dan takarar shugaban kasa na Labour Party, Peter Obi yua lashe a zaben shugaban kasa inda ya zo na uku bayan Tinubu da Atiku.
Asali: Legit.ng