“Zan Sauya Farkon Sunanka”: Zababben Shugaban Kasa Tinubu Ga Gwamna Atiku Bagudu
- Bola Ahmed Tinubu, zababben shugaban kasa na zaben 2023 ya bayyana matakin da zai dauka a kan sunan gwamnan jihar Kebbi
- Tinubu ya bayyana cewa zai sauyawa Gwamna Atiku Bagudu farkon sunansa saboda jajircewar da ya yi wajen ganin nasarar jam'iyyarsu a zaben
- Bagudu dai yana dauke da sunan babban abokin hamayyar Tinubu, Alhaji Atiku Abubakar na jam'iyyar PDP
Zababben shugaban kasar Najeriya, Bola Tinubu, ya bayyana cewa zai yi yunkurin sauya farkon sunan gwamnan jihar Kebbi, Atiku Bagudu.
Yayin da yake jawabin godiyarsa a safiyar ranar Laraba, 1 ga watan Maris, Tinubu ya sanar da magoya bayansa cewa gwamnan ya yi iya bakin kokarinsa don tabbatar da ganin cewa jam'iyyar APC mai mulki a zaben shugaban kasar da aka kammala.
Sunan Bagudu daya da babban abokin hamayyar Tinubu na jam'iyyar Peoples Democratic Party (PDP), Atiku Abubakar.
Tinubu ya fafata a zaben shugaban kasar na 2023 tare da Abubakar, Peter Obi na jam'iyyar Labour Party da wasu yan takara 15 daga jam'iyyun siyasa daban-daban.
DUBA: Shigo shafin Legit.ng na manhajar Legit.ng na Telegram! Kada ka bari komai ya wuce ka
Shakka babu wannan ne dalilin da yasa Tinubu yake ganin akwai bukatar sauya sunan gwamnan.
Tinubu ya ce:
"Dole zan sauya farkon sunanka."
A safiyar yau Laraba, 1 ga watan Maris ne hukumar zabe ta kasa mai zaman kanta ta ayyana Tinubu a matsayin wanda ya yi nasara a zaben shugaban kasar.
Farfesa Mahmood Yakubu ya kuma sanar da cewar INEC za ta baiwa Tinubu satifiket din lashe zabe a yau Laraba da karfe 3:00 na rana.
Fayose ya taya zababben shugaban kasa, Bola Tinubu murnar cin zabe
A wani labarin kuma, mun ji cewa tsohon gwamnan jihar Ekiti, Ayodele Fayose, ya taya Asiwaju Bola Ahmed Tinubu murnar lashe zaben shugaban kasa na 2023 da ya yi karkashin inuwar jam'iyyar APC mai mulki.
Fayose ya bukaci daukacin yan takarar shugaban kasa musamman Alhaji Atiku Abubakar na jam'iyyar PDP da su karbi sakamakon zaben saboda ra'ayin kasar da zaman lafiya.
Ya kuma bukace su da su sake gwada sa'arsu a gaba domin dai a cewarsa idan da rai akwai rabo. Fayose ya kuma bukaci shugaban jam'iyyar adawar na kasa, Iyorchia Ayu da ya sauka daga kujerarsa.
Asali: Legit.ng