Zaben 2023: Tsohon Gwamnan Gombe, Dankwambo, Ya Kayar Da APC A Kujerar Sanata

Zaben 2023: Tsohon Gwamnan Gombe, Dankwambo, Ya Kayar Da APC A Kujerar Sanata

  • Dankwambo ya kada sanata mai ci a zaben sanata mai wakiltar Arewacin Gombe ta tsakiya a zaben da ya gudana ranar Asabar
  • Tsohon gwamnan na Jihar Gombe na jam'iyyar PDP ya kayar da Alkali na jam'iyyar APC a yankin da ke da kananan hukumomi biyar
  • Dankwambo yayi takarar tun a shekarar 2019 sai dai ya sha kayi a hannun Alkali na jam'iyyar APC

Jihar Gombe - Tsohon gwamnan Jihar Gombe, Ibrahim Dankwambo, ya lashe kujerar sanata mai wakiltar Arewacin Gombe ta tsakiya, inda ya kayar da sanata mai ci, Saidu Alkali na jam'iyyar APC.

Kamfanin dillancin labarai na kasa (NAN) ya ruwaito cewa Arewacin Gombe ta tsakiya na kunshe da kananan hukumomi biyar, Gombe, Kwami, Dukku, Funakaye da Nafada.

Dankwambo
Zaben 2023: Tsohon Gwamnan Gombe, Dankwambo, Ya Kada APC A Kujerar Sanata. Hoto: Daily Trust
Asali: Depositphotos

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Kara karanta wannan

Taliyar karshe: Fitaccen sanata, Na'Allah ya rasa kujerar sanata, dan PDP ya lashe zabe

Umaru Gurama, mataimakin shugaban jami'ar tarayya ta kashere (FUK) kuma baturen zaben yankin shi ya sanar da sakamakon ranar Litinin a Malamsidi hedikwatar karamar hukumar Kwami ta Jihar Gombe.

Ya ce Dankwambo na jam'iyyar PDP ya samu kuri'a 143155 inda ya kada mai biye masa, Alkali na jam'iyyar APC, wanda ya samu kuri'a 77,948.

A cewarsa:

''Bayan cika kowacce irin ka'ida da doka ta tanada da kuma samun mafi rinjayen kuri'u, ina bayyana Alhaji Ibrahim Dankwambo a matsayin wanda ya lashe zaben kuma sabon zababben sanata.''

Baturen zaben ya ce an soke kuri'a 8,566, Premium Times ta rahoto.

Kamfanin dillancin labarai na kasa (NAN) ta ruwaito cewa Dankwambo ya yi takara a 2019 sai dai ya sha kayi a hannun Alkali.

Abdulaziz Yar'adua, kanin tsohon shugaban kasar Najeriya ya lashe zaben sanata a Jihar Katsina

A bangare guda, kun ji cewa Kanal Abdulaziz Yar'adua, kanin tsohon shugaban kasar Najeriya marigayi Umaru Musa Yar'adua ne aka tabbatar ya yi nasara a zaben dan majalisar dattawa na tsakiyar Katsina.

Kara karanta wannan

Da Dumi-Dumi: Ahmed Lawan Ya Sake Lashe Zaben Sanata a Yobe

Jaridar Premium Times ta rahoto cewa Abdul Aziz Yar'adua wanda ake yi wa lakaci da Audu Soja ya yi nasara ne karkashin inuwar jam'iyyar APC mai mulki a Katsina.

Abdulaziz Yar'adua ya samu kuri'u 153,512, sannan abokin fafatawar sa Aminu Surajo na PDP ya samu kuri'u 152,140.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aminu Ibrahim avatar

Aminu Ibrahim (Hausa HOD) Aminu Ibrahim leads the Hausa Desk at Legit.ng. He holds a Bachelor's degree in Microbiology from Ahmadu Bello University, Zaria, and pursued further with a Master's degree in Environmental Microbiology from Federal University Dutse, Jigawa. With over seven years of experience, Aminu has honed his craft in news reporting and content editing, weaving narratives that captivate and inspire audiences: aminu.ibrahim@corp.legit.ng or +2348030996164