Yanzu Yanzu: Gwamnonin Enugu Da Cross River Sun Fadi Zaben Sanata
- Gwamnan PDP, Ifeanyi Ugwuanyi ya sha kaye a zaben Sanata inda dan takarar Labour Party, Okechukwu Ezea ya ci zabe a jihar Enugu
- Hakazalika, Gwamna Ben Ayade na jihar Cross River bai yi nasara ba a kokarinsa na son komawa majalisar dattawan Najeriya
- Ayade wanda ya kasance dan APC ya sha kaye a hannun sanata mai ci, Jarigbe Agom-Jarigbe
Gwamna Ifeanyi Ugwuanyi na jihar Enugu ya fadi takarar zaben sanata inda dan takarar jam'iyyar Labour Party, Okechukwu Ezea ya yi nasara, rahoton Premium Times.
Mista Ugwuanyi, wanda ke kammala wa'adinsa na biyu a matsayin gwamna ya kasance dan takarar jam'iyyar PDP a zaben sanata mai wakiltan Enugu ta arewa a zaben ranar Asabar, 25 ga watan Fabrairu.
Baturen zaben, Chukwuemeka Ubaka, ne ya sanar da sakamakon a cibiyar tattara zabe na hukumar zabe ta kasa mai zaman kanta da ke karamar hukumar Nsukka a ranar Litinin.
Gwamnan Cross River ya fadi zaben sanata
Daily Trust ta kuma rahoto cewa Gwamna Ben Ayade na jihar Cross River ya fadi a kokarinsa na komawa majalisar dattawa inda ya sha kaye a hannun sanata mai wakiltan Cross River ta arewa, Sanata Jarigbe Agom-Jarigbe.
DUBA: Shigo shafin Legit.ng na manhajar Legit.ng na Telegram! Kada ka bari komai ya wuce ka
Ayade wanda ya yi sanata tsakanin 2011 da 2015 ya sha kaye a zaben na ranar Asabar da kuri'u 56,595, ya sha kaye a hannun Agom-Jarigbe na PDP wanda ya samu kuri'u 76,145.
Baturen zabe a jihar, Dr Emmanuel Emanghe, wanda ya yi jawabi a madadin hukumar INEC ya sanar da sakamakon zaben da misalin karfe 3:05 na tsakar dare wayewar garin Litinin.
Ayade ya kammala wa'adinsa na biyu a matsayin gwamnan jihar Cross River don haka ya shiga tseren kujerar sanata mai wakiltyan yankin Cross River ta arewa.
Asali: Legit.ng