Tinubu Ya Lashe Kananan Hukumomi 15 Da Aka Sanar Kawo Yanzu
Dan takara shugaban kasa na jam'iyyar All Progressives Congress (APC) Bola Tinubu, ya kayar da dukkan abokan hamayyarsa a zaben kananan hukumomi 15 da aka sanar a jihar Ekiti da Ondo.
Tinubu ya lallasa Atiku Abubakar, Rabiu Kwankwaso da Peter Obi.
Yayinda ya samu kuri'u 187,896 daga kananan hukumomin 15, mai biye masa shine Atiku Abubakar na jam'iyyar Peoples Democratic Party (PDP) wanda ya samu kuri'u 71,423 yayinda Peter Obi na jam'iyyar 9,789. Shi kuwa Rabiu Kwankwaso yana da jimillar kuri'u 248.
A sanarwar da aka yi misalin karfe 7 na safiyar Lahadi a cibiyar tattara kuri'u dake babbar binrin jihar, Ado Ekiti.
Na Ondo kuwa an yi shi ne misalin karfe 11 a Akure.
Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!
Ga sakamakon da aka sanar:
Jiha Ekiti
1. Karamar hukumar Oye
APC - 14472
LP - 643
NNPP - 20
NRM - 13
PDP - 7,143
2. Karamar hukumar Ilejemeje, jihar Ekiti.
APC - 4,599
LP - 97
NNPP - 03
PDP - 2,662
3. Karamar hukumar Efon Alaaye
APC - 5,873
LP - 125
NNPP - 03
PDP - 2,521
4. Ƙaramar hukumar Gboyin
APC - 11,969
LP - 245
NNPP - 11
PDP 4,178
5. Karamar hukumar Ijero
APC - 12,628
LP - 373
NNPP- 06
PDP - 5,731
6. Karamar hukumar Ikere
APC - 11,659
LP - 910
NNPP - 24
PDP - 7,198
7. Karamar hukumar Ise-Orun
APC - 11,415
LP - 497
NNPP - 10
PDP - 2734
8. Karamar hukumar Ido/Osi
APC - 11917
LP - 782
NNPP - 14
PDP - 7476
9. Karamar hukumar Irepodun/Ifeodun
APC - 14265
LP - 544
NNPP - 24
PDP - 5516
10. Karamar hukumar Ekiti ta yamma
APC - 14516
LP - 391
NNPP - 10
PDP - 4318
11. Karamar hukumar Moba
APC - 12,046
LP - 246
NNPP - 11
PDP - 5847
12. Karamar hukumar Ikole
APC - 15465
LP - 779
NNPP - 11
PDP - 10,198
Jihar Ondo
Karamar hukumar Akure North
APC - 14,261
PDP -4,633
LP - 2,945
NNPP: 66
Karamar hukumar Akoko South East
APC - 10,765
PDP - 3,016
LP - 470
NNPP: 07
Karamar hukumar Akoko South West.
APC - 28,367
PDP - 5,376
LP - 920
NNPP — 28
Powered
INEC na Barazanar Soke Zaɓukan Jihar Kogi, Biyo Bayan Masu Matsaloli da Aka Samu.
A wani labarin kuwa, INEC tayi barazanar soke zaɓen jihar Kogi sakamakon tashe -tashen hankula da aka samu yayin gudanar da zaɓukan a Kogi.
Dr Hale Longpet, shine Kwamishinan Zaɓe na jihar Kogi. Kuma shine ya tura saƙon yiwuwar hakan lokacin da yake maida martani abisa rigimar data ɓarke a wasu ƙananan hukumomi na jihar.
Tunda fari dai, an samu rahotannin wasu yan jagaliyar siyasa ne da suka shiga guraren akwatunan zaɓe a Anyigba da Dekina dake gabashin Kogi suka aikata ta'annati.
Sannan a Mopa dake Kogi ta yamma da kuma wasu sassa na Kogi ta tsakiya an samu makamancin irin wannan balahirar yayin da wasu ɓata gari sukayi awon gaba da akwatunan zaɓe zuwa wuraren da ba'a sani ba.
Asali: Legit.ng