An Bindige Mata Biyu a Bayelsa Yayin da Rikicin Zabe Ya Kaure a Ribas
- Wasu bata gari sun harbi mata biyu yayin zaben shugaban kasa a gudunmar Ofoni ta jihar Bayelsa
- Dandazon masu zabe sun cafke biyu daga cikin matasan da suka yi harbi inda suka mika su ga yan sanda
- A jihar Ribas, rikicin zabe ya kaure a wasu kananan hukumomi bayan wasu mutane sun tilastawa jama'a zabar yan takarar da suke so
Rahotanni sun kawo cewa wasu mata biyu sun jikkata sakamakon harbin bindiga yayin da rikici ya barke a gudunmar Ofoni da ke mahaifar mataimakin gwamnan jihar Bayelsa, Sanata Lawrence Ewhrudjakpo, yayin zaben shugaban kasa.
Wani ganau wanda ya je kada kuri'a a rumfar zaben, ya bayyanawa jaridar Daily Trust a ranar Lahadi cewa wasu fusatattun matasa uku daga garin sun harbi wata matashiya kan wani sabani da ya gibta a tsakaninsu.
Kamar yadda ya bayyana, faruwan al'amarin ya kawo tsaiko a tsarin gudanar da zabe a yankin.
A cewarsa, harbin ya sake samun wata mata mai matsakaicin shekaru inda aka gaggauta daukarta zuwa wani asibiti da ke kusa.
DUBA: Bibiyemu a Instagram don samun labarai masu muhimmanci kai tsaye cikin manhajar
An tattaro cewa dandazon jama'ar da ke wajen sun kama biyu daga cikin yan daban da suka kawo hatsaniyar sannan suka mika su ga jami'an tsaro.
Yadda lamarin zabe ya kasance a jihar Ribas
A Ribas, an tattaro cewa rikici ya barke a wasu kananan hukumomin jihar. An tattaro cewa jam'iyyar siyasa mai jagoranci a jihar ta ci zarafin wasu masu zabe kan wani dan takara da suke so a zaba.
Jaridar Punch ta kuma rahoto cewa wata tawagar yan sanda ta kama wakilinta, Gbenga Oloniniran a kusa da gidan Gwamna Nyesom Wike in Rumuiprikon, karamar hukumar Obio/Akpor ta jihar.
Oloniniran, wwanda ya je aikin zabe yana ta daukar hotunan inda jami'an yan sanda ke kama wasu matasa a wata rumfar zabe lokacin da jami'an tsaron suka damke shi.
Mutane biyar sun jikkata a harin Gwoza, In ji Yan sandan jihar Borno
A wani labarin kuma, rundunar yan sandan jihar Borno ta bayyana cewa mutane biyar ne suka jikkata sakamakon harin da kungiyar ta'addanci suka kai kan masu zabe a yankin Gwoza.
Asali: Legit.ng