Kwankwaso Ya Samu Nasara Ta Farko, Ya Lashe Akwatinsa, Atiku ya Tashi a Babu Ko 1

Kwankwaso Ya Samu Nasara Ta Farko, Ya Lashe Akwatinsa, Atiku ya Tashi a Babu Ko 1

  • Sanata Rabiu Musa Kwankwaso ya samu nasarar farko a zaben bana, ya lashe akwatin da ya kada kuri'a
  • Kwankwaso ya lallasa abokan hamayyarsa da tazara mai fadi a rumfarsa ya gundumar Kwankwaso
  • Har yanzu ana cigaba da tattaro sakamakon zaben kuri'an da aka kada a fadin tarayya

Dan takarar shugaban kasa na jam'iyyar New Nigerias Peoples Party NNPP, Injiniya Rabiu Musa Kwankwaso ya samu nasara a akwatin da ya kada kuri'a yau a Kwankwaso, karamar hukumar Madobi ta jihar Kano.

Kwankwaso ya kada kuri'arsa a rumfar zabe ta Tandu PU002, Ajiya, gundumar Kwankwaso, karamar hukumar Madobi ta jihar.

Kwankwaso
Kwankwaso Ya Samu Nasara Ta Farko, Ya Lashe Akwatinsa, Atiku ya Tashi a Babu Ko 1
Asali: Original

Kwankwaso ya kada kuri'arsa tun da safe kuma ya lallasa Bola Ahmed Tinubu na jam'iyyar APC, Atiku Abubakar na Jam'iyyar PDP da kuma Peter Obi na jam;iyyar LP.

DUBA: Shigo shafin Legit.ng na manhajar Legit.ng na Telegram! Kada ka bari komai ya wuce ka

Kara karanta wannan

Atiku Ya Ba Da Mamaki, Ya Lallasa Bola Tinubu a Akwatin Gidan Gwamnatin Kaduna

Wanda ya biyo masa shine Tinubu wanda ya samu kusan rabin kuri'un da Kwankwaso ya samu.

Atiku na PDP kuwa ko kuri'a 1 tak bai samu hakazalika Peter Obi .

Kalli sakamakon:

PU002, Tandu, Kwankwaso, Madobi LGA

APC: 112

PDP: 0

LP: 0

NNPP: 284

Atiku ga lallasa Tinubu a gidan gwamnatin Kaduna

A wani labarin kuwa, Mai neman zama shugaban kasa a inuwar PDP, Alhaji Atiku Abubakar, ya samu nasara kan abokin hamayyarsa na APC, Bola Tinubu, a ɗaya daga cikin rumfunan gidan gwamnatin Kaduna, PU 013.

APC - 40

LP - 48

PDP - 69

NNPP - 11

Asali: Legit.ng

Authors:
AbdulRahman Rashida avatar

AbdulRahman Rashida