Tashin Hankali A Imo Yayin Da Dan Majalisar PDP Ya Tsallake Rijiya Da Baya A Wani Farmaki
- A ranar zabe, Asabar, 25 ga watan Fabrairu, dan majalisar wakilai na tarayya na jam'iyyar PDP ya yi sabon korafi
- Honarabul Uju Kingsley Chima ya yi ikirarin cewa rayuwarsa na cikin babban hatsari bayan yunkurin kashe shi da wasu yan bindiga suka yi a jihar
- Wannan bayanin ya fito ne a cikin wata sanarwa da sakataren watsa labarai na PDP a jihar Imo, Collins Opurozor ya fitar
Jihar Imo - Jam'iyyar Peoples Democratic Party, PDP, a jihar Imo ta bayyana damuwa matuka kan ran daya cikin dan takarar ta a jihar Imo.
Hakan na zuwa ne a ranar Asabar, 25 ga watan Fabrairu, yayin da dan takarar ya koka kan cewa wasu yan bindiga a jihar sun yi yunkurin halaka mamba na majalisar wakilai na tarayyya mai wakiltar Ohaji-Egbema, Oguta da Oru West, Honarabul Uju Kingsley Chima, The Punch ta rahoto.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Chima kuma shine dan takarar jam'iyyar PDP na mazabar a zaben yau, Asabar, 25 ga watan Fabrairu.
Sanarwa da sakataren watsa labarai na PDP a jihar Imo, Collinsa Opurozor ya fitar ta ce ya tsallake rijiya da baya sau biyu a harin da aka kawo masa a daren Juma'a, 24 ga watan Fabrairu.
"Jam'iyyar mu na son sanar da yan Najeriya cewa a cikin kwana uku da suka gabata, dan takarar mu ya tsallake rijiya da baya a farmaki biyu da aka kai masa. A yayin da ya ke kammala kamfen dinsa a Umuapu a Ohaji-Egbema, kwana uku da suka shude, wasu yan ta'adda sun iso wurin sun kai wa dan takarar mu hari, har da mambobin jam'iyya da mutanen Imo.
"Har yanzu, hare-haren bai tsaya ba, domin akwai motar yaki a kofar gidansa kuma yan ta'addan suna cin karensu ba babbaka. Hakan na faruwa a jihar Imo a ranar zabe!."
Dakaci karin bayani ...
Asali: Legit.ng