Shugaba Buhari Yayi Allah Wadai Da Kisan Ɗan Takarar Sanatan Labour Party
- Shugaban ƙasa Muhammadu Buhari yayi magana kan mummunan kisan da aka yiwa wani ɗan takarar sanata
- Shugaban ƙasar yayi Allah wadai da kisan sannan ya aike da saƙon ta'aziyyar sa ga iyalan ɗan takarar
- Shugaba Buhari ya ba jami'an tsaro wani muhimmin umurni kan waɗanda suka aikata mummunan laifin
Abuja- Shugaban ƙasa Muhammadu Buhari, yayi Allah wadai da mummunan kisan d aka yiwa ɗan takarar sanatan Enugu ta Gabas, na jam'iyyar Labour Party (LP) Cif Oyibo Chukwu da hadimin sa.
Shugaban ƙasar ya bayyana hakan ne a wata sanarwa da hadimin sa na musamman a ɓangaren midiya, Femi Adesina, ya fitar a ranar Juma'a. Rahoton Arise News
Shugaba Buhari yace waɗanda suka aikata wannan mummunan aikin basu san daraja da ƙima ta ran ɗan Adam ba, saboda haka sun cancanci su fuskanci adaba mai tsanani.
Shugaba Buhari ya kuma ƙara tabbatar da cewa har yanzu yana nan a kan bakansa na ganin an gudanar da tsaftataccen zaɓe wanda babu tashin hankali a cikin sa.
DUBA: Shigo shafin Legit.ng na manhajar Legit.ng na Telegram! Kada ka bari komai ya wuce ka
Ya ƙara tunawa ƴan siyasa cewa zaɓin masu zaɓe shine abinda yake da muhimmanci, sannan ƴan Najeriya da suka cancanci zaɓe su fito su kaɗa ƙuri'un su ba tare da wata fargaba ba.
Shugaban ƙasar ya kuma bayar da umurni ga jami'an tsaro da su tabbatar sun gano waɗanda suka aikata wannan mummunan ta'addancin. Rahoton jaridar Thisday
Ya kuma miƙa saƙon ta'aziyyar sa ga iyalan waɗanda harin ya ritsa da su, ƙungiyar lauyoyi ta ƙasa da jam'iyyar Labour Party.
Yan Bindiga Sun Sace Matar Basarake a Jihar Imo, Sun Kone Gidajen Shugabannin APC da LP
A wani labarin na daban kuma, miyagun ƴan bindiga sun sace matar wani basarake a jihar Imo, sannan suka farmaki gidajem shugabannin jam'iyyun APC da Labour Party.
Wasu miyagun yan bindiga sun sace matar basaraken Amuro na karamar hukumar Okigwe a jihar Imo, Uzoeze Umugborogu. Mummunan harin ya auku nr a ranar Laraba.
Bayan sace matar basaraken, tsagerun ‘yan bindigan sun kuma kone gidajen shugabannin jam’iyyun APC da LP na gundumar Amuro.
Asali: Legit.ng