Fadar Shugaban Kasa: Shugaban APC, Adamu, Ya Yi Magana Kan 'Kabal' Na Aso Rock
- Shugaban jam'iyyar APC na kasa, Abdullahi Adamu, ya karya batun masu yin zagon kasa ga dan takarar jam'iyyar, Bola Tinubu, a fadar shugaban kasa
- Adamu ya bayyana cewa mugu shi yasan makwantar mugu, kuma tun da fadar shugaban kasa ta karyata batun, shi ya yarda da fadar shugaban kasar
- Nasir Elrufai, ya yi ikirarin masu zagon kasar a tattaunawa da dama, amma shugaban APC na kasa ya ce ba shi da masaniya
FCT, Abuja - Abdullahi Adamu, shugaban jam'iyyar All Progressives Congress, APC, ya karyata batun wasu maso zagon kasa a fadar shugaban kasa da ke aiki don kayar da Tinubu, dan takarar shugabancin kasa na jam'iyyar.
Shugaban jam'iyya mai mulkin ya bayyana haka ne lokacin da yake martani ga kalaman gwamnan Jihar Kaduna, Nasir El-Rufai, Jaridar Tribune ta ruwaito.
DUBA: Shigo shafin Legit.ng na manhajar Legit.ng na Telegram! Kada ka bari komai ya wuce ka
A tattaunawa daban daban, El-Rufai ya zargi yan takarar masu zagon kasan sun sha kayi a hannun Tinubu lokacin zaben fitar da gwani na jam'iyyar kuma hakan ya jawo su ke adawa da tsohon gwamnan na Jihar Lagos.
Abin da ke faruwa a baya-bayan kan APC, Bola Tinubu, Abdullahi Adamu, Nasir El-Rufai, Zaben 2023, Shugaban Muhammadu Buhari
Amma Adamu, da ya ke martani, ya ce ba shi da masaniya akan maso zagon kasar a fadar shugaban kasar.
Ya bayyana cewa mutane su kan yi irin wadannan kalamai idan ba su samu yadda suke so ba ko kuma wanda suka fi su suka yi rinjaye akan wani abu da suke nema.
Shugaban ya ce:
''Maganar masu zagon kasa a fadar shugaban kasa, to, ni bana cikin miyagu, kuma mugu shi yasan makwantar mugu. Ni bana cikin su.
Ban san batun wani zagon kasa ba. Ina dai ji kuma ina karantawa a jaridu, amma fadar shugaban kasa ta karyata.
Ba a fadar shugaban kasa na ke aiki ba, amma na yarda da su, kuma na gamsu sosai cewa babu wani mai zagon kasa a fadar shugaban kasa.''
Naja'atu Mohammad ta yi ikirarin cewa Aisha Buhari na daga cikin masu hana ruwa gudu a fadar shugaban kasa
A wani rahoton, kun ji cewa tsohuwar mataimakiyar direkta na kwamitin yakin neman zaben shugaban kasa na APC, Naja'atu Mohammed ta yi ikirarin cewa Aisha Buhari, matar shugaban kasa na cikin wadanda suke hana ruwa gudu a fadar shugaban kasar da ake kira 'cabal'.
Naja'atu ta yi wannan maganan ne yan kwanaki bayan gwamnan jihar Kaduna Nasir El-Rufai shima ya ce akwai wasu masu kitse-kitse da nufin yi wa Tinubu zagon kasa a zaben 2023 a fadar shugaban kasa.
Asali: Legit.ng