Shugaban APC Yace Jam'iyyar Zata Yi Nasara a Zaɓen Ranar Asabar

Shugaban APC Yace Jam'iyyar Zata Yi Nasara a Zaɓen Ranar Asabar

  • Shugaban jam'iyyar All Progressives Congress (APC) ta ƙasa ya bayyana cewa nasara ta su ce a zaɓen dake tafe
  • Abdullahi Adamu ya bayyana dalilin da ya sanya yake jin cewa jam'iyyar su zata yi nasara a zaɓen
  • Shugaban jam'iyyar ya kuma yi wani muhimman kira ga magoya bayanta da sauran jam'iyyun adawa

Abuja- Shugaban jam'iyyar APC ta ƙasa, Abdullahi Adamu, yace jam'iyyar tayi aiki tuƙuru sannan ta cancanci ta samu nasara a babban zaɓen ƙasar nan.

Adamu ya bayyana hakan ne a birnin tarayya Abuja a ranar Laraba, yayin tattaunawa da ƴan jarida. Rahoton The Cable

Adamu
Shugaban APC Yace Jam'iyyar Zata Yi Nasara a Zaɓen Ranar Asabar Hoto: Vanguard
Asali: UGC

Yace jam'iyyar ta shirya tsaf domin tunkarar zaɓen na ranar Asabar.

“Mu a wajen mu, sakamakon nasara kawai muke tsammani daga wannan zaɓen. Mun yi aiki tuƙuru sosai." A cewar sa

Kara karanta wannan

"Mun Gano Su" Jam'iyyar PDP Ta Fallasa Shirin El-Rufa'i Na Siyan Ƙuri'a a jihar Kaduna

DUBA: Shigo shafin Legit.ng na manhajar Legit.ng na Telegram! Kada ka bari komai ya wuce ka

"Babu jam'iyyar da tayi gagarumin yaƙin neman zaɓe irin wanda jam'iyyar APC tayi."

Shugaban yace yana da tabbacin cewa ƙoƙarin da suka yi zai haifi ɗa mai ido.

“Ina da tabbacin cewa ƙoƙarin da mu kayi wajen yaƙin neman zaɓe zai sanya mu samu nasara a zaɓen."
“Sannan da yardar Allah jam'iyyar tabbas zamu yi nasara a zaɓen ranar Asabar na shugaban ƙasa."
"A lokacin yaƙin neman zaɓen mu, duk inda muka je dandazon mutane na fitowa domin tarbar mu, hakan ya tabbatar da cewa jam'iyyaru babu kamar ta a Najeriya."
“Ina da tabbacin cewa abinda na gani a lokacin da muke zaga ƙasar nan, jam'iyyar APC zata samu nasara a zaɓen ranar Asabar."

Adamu yayi kira da magoya bayan jam'iyyar da wakilan akwatuna da su zauna lafiya da kowa sannan su jajirce yadda yakamata a lokacin zaɓen. Rahoton Punch

Kara karanta wannan

Abu Ɗaya Ne Tak, Abinda Inyamurai Zasu Yi Domin Samun Shugabancin Najeriya, Sanatan APC

Ya kuma yi kira ga sauran jam'iyyu da su marawa hukumar zaɓe mai zaman kanta (INEC) baya domin gudanar da sahihin zaɓe.

A wani labarin na daban kuma, ƙungiyar malaman Kano ta bayyana ɗan takarar da take marawa baya a zaɓen shugaban ƙasa.

Sai dai ƙungiyar tace a zaɓen gwamna bata goyon bayan kowane ɗan takara.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sharif Lawal avatar

Sharif Lawal Sharif Lawal ma'aikacin jarida ne wanda ya samu gogewa a harkar aikin jarida. Ya yi digirinsa na farko a jami'ar Ahmadu Bello (ABU) da ke Zaria. Ya samu horo daga Reuters kan aikin jarida da tantance labarai. Za a iya tuntubarsa ta Sharif.lawal@corp.legit.ng