2023: Jigon APC Ya Bayyana Tasirin Da Sauyin Naira Zai Yi Ga Nasarar Tinubu
- Sanata Orji Uzor Kalu, bulaliyar majalisar tarayya ya ce sabon tsarin sauya fasalin takardun naira ba zai kawo cikas ga nasarar Bola Tinubu ba
- Tsohon gwamnan na jihar Anambra ya ce yana kyautata zaton APC za ta ci zaben shugaban kasar na ranar 25 ga watan Fabrairu saboda yawan magoya bayansu a kasar
- Kalu ya kuma ce idan da shine ke matsayin Shugaba Muhammadu Buhari zai yi biyayya ga umurnin kotun koli na cigaba da amfani da tsaffin kudi tare da sabbin
Bulaliyar majalisar dattawa, Sanata Orji Kalu, ya ce sabuwar tsarin sauya fasalin naira da babban bankin kasa, CBN, ya fito da shi ba zai shafi yiwuwar samun nasarar dan takarar shugaban kasa na jam'iyyar All Progressives Congress, APC, Bola Ahmed Tinubu ba a zaben ranar 25 ga watan Fabrairu.
Tsohon gwamnan na jihar Anambra ya bayyana hakan ne a wata hira da aka yi da shi a shirin Politics Today na gidan talabijin na Channels.
Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!
Ya ce Tinubu ne shugaban kasar Najeriya na gaba kuma babban kwamandan dakarun Jamhuriyyar Tarayyar Najeriya, Daily Trust ta rahoto.
Sauya naira ba zai shafi nasarar Tinubu ba domin muna da magoya baya masu yawa, Orji Kalu
Da aka masa tambaya ko tsarin sauya nairan zai shafi damar nasarar Tinubu, Kalu ya ce:
"A'a, Tinubu shine Tinubu kuma duk wanda ya yi tsarin shima shine ya ya san kansa.
"Kotun koli ta riga ta yanke hukunci kuma mu a wurin mu, shugaban jam'iyyar mu na kasa wanda kuma tsohon takwara na ne a matsayin gwamna duk ra'ayin mu daya kan batun.
"Idan ni ke matsayin shugaban kasa, da zan yi biyayya ga umurnin kotun koli. Mun fi yawa kuma mune ke babban inuwa. Mu za mu lashe zaben.
"Tinubu shine shugaban kasa na gaba kuma babban kwamandan sojojin Najeriya. Abin da ya bani kwarin gwiwa shine muna da magoya baya masu yawa da tallafi daga yan Najeriya."
'Yan son hana ruwa gudu ne suka janyo karancin man fetur da naira, Femi Gbajabiamila
A wani rahoton daban, kakakin majalisar wakilai na tarayyar Najeriya, Femi Gbajabiamila ya ce wasu wadanda ke son hana ruwa gudu ne suka kirkiri karancin man fetur da sabbin naira a Najeriya.
Gbajabiamila ya furta hakan ne a ranar Talata yayin jawabinsa a wurin kaddamar da shirin rabon ababen sufuri na 'Gbaja ride' a Legas.
Asali: Legit.ng