Ana Dab Da Zaɓe, Wasu Malaman Addini Sun Koma Bayan Tinubu
- Ana dab da a fara zaɓen 2023 a Najeriya, Tinubu ya samu wani babban tagomashi a yunƙurin sa zama shugaban ƙasa
- Ɗan takarar na shugaban ƙasa a inuwar jam'iyyar APC ya samu goyon bayan wasu malaman addini
- Malaman addinin sun yi ƙarin haske kan dalilin da ya sanya suka marawa Tinubu baya a maimakon sauran ƴan takarar shugaban ƙasar
Rivers-A wani abu wanda wasu mabiya addinin kirista ba zasu yi maraba da shi ba, sama da fastoci 100 sun nuna goyon bayan su ga ɗan takarar shugaban ƙasa na jam'iyyar All Progressives Congress (APC), Asiwaju Bola Ahmed Tinubu.
Malaman addinin waɗanda suka dunƙule waje ɗaya a ƙarƙashin ƙungiyar Rivers Pastors Unite for Tinubu (RPUT), sune suka bayyana hakan bayan sun yi wata ganawa a birnin Port Harcourt. Rahoton Legit.ng
A cewar malaman addinin, Tinubu da mataimakinsa Kashim Shettima ne kaɗai za su iya ceto ƙasar nan daga ɗumbin matsalolin da take fama da su.
Kodinetan ƙungiyar RPUT, Fasto Sunday Edimeh, wanda ya bayyana matsayar da suka cimma, ya bayyana cewa babu wanda ɗan takara da ya taimaki kiristoci kamar Tinubu. Rahoton The Nation
DUBA: Shigo shafin Legit.ng na manhajar Legit.ng na Telegram! Kada ka bari komai ya wuce ka
Sai dai Edimeh yayi ƙarin haske kan cewa wannan matsayar ta su ta tsaya ne kawai akan zaɓen shugaban ƙasa, sannan bata da wata alaƙa da zaɓen gwamna da saurna zaɓukan da zaa gudanar a jihar.
Jihar Rivers na ɗaya daga cikin jihohin da jam'iyyar PDP ke da ƙarfi a Najeriya, sai dai wannan goyon baya da malaman addinin suka yi ga Tinubu zai zama wani babban koma baya ga Atiku Abubakar.
Diyar Atiku ta Zama Lauyarsa, Ta Fadi Hikimar Gwanjon Kadarorin Najeriya a Kasuwa
A wani labarin na daban kuma, ɗiyar Atiku Abubakar ɗan takarar shugaban ƙasa na jam'iyyar Peoples Democratic Party (PDP), ta fito ta kare ƙudirin mahaifin ta.
Hajiya Uwai Atiku Abubakar ta kare aniyar mahaifin ta na siyar da wasu kadarorin ƙasar nan idan ya samu ɗarewa kan kujerar madafun iko a Najeriya.
Tace hakan ba ƙaramin bunƙasa harkokin kasuwanci zai yi ba a Najeriya.
Asali: Legit.ng