Yadda Na Dakatar Da Kuɗirin Tazarcen Obasanjo -Atiku Abubakar

Yadda Na Dakatar Da Kuɗirin Tazarcen Obasanjo -Atiku Abubakar

  • Bayan dogon lokaci, Atiku Abubakar ya fito ya bayyana yadda ya kawo tarnaƙi ga kuɗirin Obasanjo na yin tazarce
  • Tsohon shugaban ƙasa Olusegun Obasanjo a baya ya taɓa neman yin tazarce karo na uku akan kujerar shugaban ƙasar nan
  • Atiku Abubakar ya bayyana hanyar da ya bi cikin sauƙi ya dakatar da wannan ƙuɗirin na tsohon shugaban ƙasar

Ɗan takarar shugaban ƙasa na jam'iyyar Peoples Democratic Party (PDP), Atiku Abubakar, ya bayyana yadda ya kawo cikas ga tazarcen da tsohon shugaban Olusegun Obasanjo, ya so yayi akan mulki.

Atiku ya bayyana kyakkyawar alaƙar da yake da ita da ƴan majalisu a lokacin yana mataimakin shugaban ƙasa, itace ta sanya shirin tazarcen Obasanjo bai yi nasara ba. Rahoton The Punch

Atiku
Yadda Na Dakatar Da Kuɗirin Tazarcen Obasanjo -Atiku Abubakar
Asali: Twitter

Yace wannan kyakkyawar alaƙar itace ta sanya da shi da wasu ƴan majalisu suka dakatar da tazarcen Obasanjo, inda yace ya ƙosa ya sake haɗa kai da ƴan majalisun bayan an zaɓe shi a shugaban ƙasa tare da nasu zaɓen a matsayin ƴan majalisu.

Kara karanta wannan

Karancin Kuɗi: Marasa Lafiya Na Shan Wuya, Magani Yayi Musu Wahalar Samu, Kungiyar Likitoci

Hakan a cewar Atiku zai sanya suyi aiki yadda yakamata tare domin ciyar da ƙasar nan gaba.

DUBA: Bibiyemu a Instagram don samun labarai masu muhimmanci kai tsaye cikin manhajar

Ɗan takarar na jam'iyyar PDP yayi wannan furucin ne a wajen wani taro da ƴan takarar kujerar ƴan majalisu a zaɓen 2023 a birnin tarayya Abuja. Rahoton Thisday

A kalamansa:

“Lokacin da nake mataimakin shugaban ƙasa, na samar da kyakkyawar alaƙa tsakani na da ƴan majalisu, wannan alaƙar itace ta sanya muka dakatar da tazarce ko yunƙurin zama din-din-din kan kujerar shugaban ƙasa wanda Obasanjo yayi.

Da yake kokawa kan matsalar tsaro d halin da tattalin arziƙin ƙasar nan yake ciki a yanzu, Atiku yace:

"Ƙasar mu ta samu kanta cikin wani lokaci mai cike da ƙalubale a tarihinta. Yanzu kawunan mu duk a rabe suke a saboda wasu abubuwa da tsare-tsaren gwamnatin APC."

Kara karanta wannan

2023: Bai San Mu Bamu San Shi Ba, Ƙungiyar Dattawan Arewa Ta Nesanta Kanta Da Takarar Atiku

"Haka kuma matsalar tsaro ta ƙara taɓarɓarewa yayin da tattalin arziƙin ƙasar yake ta tangal-tangal."

2023: Atiku Bai Kai Matsayin Samun Kuri'un Mutanen Ribas Ba, Wike

A wani labarin na daban kuma, gwamna Wike ya ƙara caccakar Atiku Abuɓakar, ɗan takarar shugaban ƙasa na jam'iyyar PDP

Wike da Atiku sun daɗe suna takun saƙa tun bayan da Atiku ya lashe zaɓen fidda gwanin shugaban ƙasa na jam'iyyar PDP

Asali: Legit.ng

Authors:
Sharif Lawal avatar

Sharif Lawal Sharif Lawal ma'aikacin jarida ne wanda ya samu gogewa a harkar aikin jarida. Ya yi digirinsa na farko a jami'ar Ahmadu Bello (ABU) da ke Zaria. Ya samu horo daga Reuters kan aikin jarida da tantance labarai. Za a iya tuntubarsa ta Sharif.lawal@corp.legit.ng