Yan Takarar Gwamnan Kano Uku Sun Janye, Sun Koma Bayan Sha'aban Sharada

Yan Takarar Gwamnan Kano Uku Sun Janye, Sun Koma Bayan Sha'aban Sharada

  • 'Yan takarar kujerar gwamnan Kano na jam'iyyu uku sun janye daga shiga zaben 2023 mai zuwa
  • Yan takarar sun sanar da cewa sun aje tikitin jam'iyyunsu, sun koma goyon bayan Sha'aban Sharada, ɗan takarar gwamna a ADP
  • Haka nan ɗan takarar mataimakin gwamna a jam'iyyar APGA, Abdussalam Gwarmai, ya bi sahun yan siyasan

Kano - 'Yan takarar gwamnan jihar Kano daga jam'iyyun siyasa uku sun janye daga takara, sun koma bayan Sha'aban Ibarahim Sharada, ɗan takarar ADP a 2023.

Jaridar Daily Trust ta rahoto cewa yan takarar da suka hakura da zama gwamna suka marawa Sharaɗa baya sun haɗa da, Furera Ahmad ta jam'iyar Booth Party (BP),

Sauran biyun su ne, Ashatu Mahmud ta jam'iyyar National Reformation Party (NRM), da kuma Ibrahim Muhammad na jam'iyyar All People’s Party (APP).

Kara karanta wannan

Ta Karewa Atiku, Bola Tinubu Ya Samu Gagarumin Goyon Baya a Arewa Kwana 5 Gabanin Zaben 2023

Jam'iyyar ADP.
Yan Takarar Gwamnan Kano Uku Sun Janye, Sun Koma Bayan Sha'aban Sharada Hoto: dailytrust
Asali: UGC

Haka zalika, ɗan takarar mataimakin gwamna na jam'iyyar APGA, Abdussalam Gwarmai, ya janye daga burinsa na takara ya koma gidan Sharaɗa a yunkurinsa na ceto Kano.

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Da yake karban yan siyasan, Sha'aban ya yi maraba da yunkurin 'yan takarar gwamna uku na haɗa karfi da karfe wajen ceto jihar Kano kuma ya yi alkawarin dawo da komai kan hanya idan ya ci zaɓe.

Ya ce zai yi garambawul a tsarin ma'aikatan Kano ta hanyar amfani da abu biyu, kyauta da hukunci, ya kuma kara da cewa za'a bude sabon shafin yanar gizo domin tallafawa Kanawa 50,000.

Ɗan takarar gwamnan ADP ya kuma kalubalanci gwamnatin Ganduje ta fito ta yi wa 'yan Kano bayanin me aka yi da makudan kuɗin da gwamnatin shugaban kasa, Muhammadu Buhari, ta ba jihohi.

Meyasa yan takarar gwamnan suka hakura?

Kara karanta wannan

Rikici: Saura kwana 6 zabe, an harbe jigon APC a wurin taron kamfen a wata jihar PDP

A nasu ɓangaren, 'yan takarar gwamnan da suka sauya sheƙa zuwa ADP sun bayyana cewa sun ɗauki wannan matakin ne saboda abinda suka hango a tattare da Sharada.

A cewarsu ganin yadda Sha'aban Sharada ke tallafawa mata da marayu da kuma kyakkyawar niyyarsa ga Kano ya sa suka aje takara domin su taimaka masa ya kai ga nasara.

A wani labarin kuma Mambobin LP A Arewa Maso Yamma Sun Watsar da Obi, Sun Koma Bayan Tinubu a 2023

Yan takarar gwamna, Majalisar dattawa, majalisar wakilai da majalisar dokokin jihar na LP a shiyyar sun ayyana goyon bayansu ga Tinubu.

A cewarsu, zasu yi aiki tukuri domin tabbatar da jam'uyyar APC ta yi nasara a zaɓen 25 ga watan Fabrairu, 2023.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262