Kai Tsaye: Bayanai Kan Yadda Kamfen Tinubu/Shettima Ke Gudana Yau A Maiduguri

All posts
Key Events
Analysis
Exclusive
6 Posts
Sort by
Our live updates have concluded for the day. Catch up on everything you missed below.
daga AbdulRahman Rashida

Jawabin Tinubu a taron

Dan takarar shugaban kasa na APC< Bola Ahmed Tinubu, ya gabatar da jawabinsa a filin kamfen.

Tinubu ya yi alkawarin farfado da tattalin arzikin Najeriya.

Yace:

"Mungode Borno kun yi mana hallaci. Zamu farfado da tattalin arziki, zamu kawo cigaba Najeriya."
"Wadanda suka san Legas, zasu iya banbanta tsakanin abinda muka samu a 1999."
"Gwamnatinmu ta al'umma ce, zamu kula da dukkanku. Farin cikinku ya zo, cigaba ya zo, and ina tabbatar muku cewa gwamnatinmu ta al'umma ce, don al'umma zatayi kuma al'umma zata zabe ta."
"Dukkanku na bukatar ingantaccen ilimi. Ilimi shine makami mafi girma saboda 'yayanku zasu amfana rana gobe."
"Ina fatan ranar Asabar, 25 ga Febriaru, 2023 zaku yi zabe."

daga AbdulRahman Rashida

Wasu sun sauya sheka daga jam'iyyun adawa zuwa APC

Shugaban uwar jam'iyyar ya karbi wasu sabbin masu sauya sheka zuwa jam'iyyar APC.

Sun hada da dan takarar kujerar Mataimakin gwamnan jihar karkashin jam'iyyar NNPP, dan takarar kujerar majalisar wakilai na NNPP, Muhammad Habib Kashim da Shugaban jam'iyyar PDP na karamar hukumar Kaga, Bilai Ali.

Hakazalika akwai Sakataren shirye-shirye na PDP, dan takarar majalisar Bayo, da kuma da Marte, Jidda Aji.

daga AbdulRahman Rashida

Jawabin Shugaban Uwar Jam'iyyar APC, Abdullahi Adamu

Shugaban Uwar Jam'iyyar APC, Abdullahi Adamu, ya bayyana cewa Allah ya riga ya baiwa jam'iyyar APC nasara a zaben 2023.

Abdullahi Adamu yace:

"Zamu ci zaben nan. Idan Allah ya yarda Asabar mai zuwa muna jiran rantsuwa ne kawai."

daga AbdulRahman Rashida

Jawabin Shettima

Dan takarar mataimakin shugaban kasa, Kashim Shettima ya gabatar da jawabinsa ga al'ummar jihar Borno.

Shettima dai ya mulki jihar Borno tsawon shekaru takwas matsayin gwamnan jihar.

Ya fara jawabi da Hausa sannan kuma ya juya Kanuri.

A karamin jawabin da yayi da Hausa, ya bayyana cewa:

Ba abinda zan ce illa Allah ya saka da alheri
Insha Allah zamu rike amana.
Zamu karfafa batun samun mai a tafkin Chadi.

daga AbdulRahman Rashida

Yadda Tinubu ya shiga filin kamfe

Jama'a sun tarbi Bola Ahmed Tinubu tare da Kashim Shettima a cikin birnin Maiduguri.

daga AbdulRahman Rashida

Masoya APC na zaman jiran Tinubu

Daruruwan masoya jam'iyyar APC sun isa filin taron suna jira zuwan dan takarar shugaban kasa APC, Bola Ahmaed Tinubu.

Tinubu dai tun daren jiya ya dira Maiduguri don halartan kamfen.'

Birni
Kai Tsaye: Bayanai Kan Yadda Kamfen Tinubu/Shettima Ke Gudana Yau A Maiduguri
Source: Twitter

Birni
Kai Tsaye: Bayanai Kan Yadda Kamfen Tinubu/Shettima Ke Gudana Yau A Maiduguri Hoto: @TheNationNews
Source: Twitter

Borno
Kai Tsaye: Bayanai Kan Yadda Kamfen Tinubu/Shettima Ke Gudana Yau A Maiduguri Hoto: @TheNationNews
Source: Twitter